Menu

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kwaso ƴan ƙasar da suka maƙale a Dubai da India

Nigeria Flags Hoton alama

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Hukumomi a Najeriya na ci gaba da aikin kwaso ɗaruruwan 'yan ƙasar da suka maƙale a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma ƙasar Indiya. 'Yan Nijeriya sama da 500 ne suka sauka a Abuja jiya Lahadi, bayan sun je Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a matsayin baƙin haure amma suka gamu da matsaloli a can. Lamarin na zuwa ne sa'o'i bayan wata sanarwa da ke cewa ƙasar da ke Gabas Ta Tsakiya ta dakatar da bai wa 'yan Najeriya biza. Hukumomi a ƙasar sun ce 'yan ƙasar da ake kwasowa daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa gida, sun fuskanci matsaloli game da dokokin shige da fice a can. Kuma ba su da kuɗin jirgi da za su biya, su koma gida. Haka zalika, ba su da cikakkun takardun zama a ƙasar. Daga ciki kuma akwai waɗanda hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke jin suna da yiwuwar aikata laifi, idan suka ci gaba da zama. Jami'ai sun ce za a ci gaba da aikin kwaso ƙarin waɗanda suka maƙale bayan isowar sawun farko na 'yan Najeriya 542 da subahin farko a ranar Lahadi. Bashir Idris Garga, babban jami'in kai ɗauki ne a NEMA, ɗaya daga cikin hukumomin da suke aikin kwaso 'yan Najeriyar kuma ya shaida wa BBC cewa ba wai ƴan Najeriya da ke Dubai bane kaɗai, akwai wasu da ke India da su ma za a kwaso su. Matakin izo ƙeyar 'yan Najeriyan na zuwa ne jim kaɗan bayan rahotannin cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da bai wa 'yan Nijeriya biza. Gwamnatin Najeriya dai ba ta ce uffan kan wannan lamari ba zuwa yanzu. Sai dai, wani ɗan Najeriya mazaunin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Qaddam Siddiq Isah ya ce batun iza ƙeyar baƙin hauren ba 'Yan Nijeriya kawai ya shafa ba, inda ya ce baya-bayan nan an izo ƙeyar 'yan ƙasashen Uganda da Ghana. Tuni dai aka fara kokawa a Najeriya game da illolin da matakin dakatar da bai wa 'yan ƙasar biza da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ɓullo da shi. Cikin 'yan kasuwar da suka fara bayyana damuwa har da kamfanonin shirya tafiye-tafiyen jirgin sama. Yakubu Umar Gilaso yana daga cikin masu shirya tafiya ne zuwa ƙasashen waje irinsu Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuma ya shaida wa BBC cewa wannan matakin ya zo masu da ba zata sakamakon akwai mutane da dama wadanda suka shirya zuwa wannan ƙasa amma a cewarsa lamarin zai jawo musu cikas. Mutane da yawa za su ci gaba da zuba ido su ji yadda hukumomin ƙasashen biyu za su ɓullo wa wannan zagaye na rikicin diflomasiyya, wanda ba su daɗe da shawo kan taƙaddamarsu ta baya ba a ƙarshen watan Agusta. Ƙasashen biyu dai a cewar bayanai na gudanar da ɗumbin harkokin tattalin arziƙi da na kasuwanci a tsakaninsu.

Source: BBC