BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Garin da ba a yunwa a Indiya

62614817 Hoton alama

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Birnin Amritsar da ke arewacin Indiya ,ya kasance cibiyar masu addinin Sikh, wanda ya yi fice kan irin taimakon da ake na ciyar da abinci ga mutum 100,000 a kowacce rana.

Birnin wanda ke da mazauna miliyan biyu, ya yi fice a fannoni da damar kamar: Dafa abinci mai daɗi da abubuwa na tarihi, da kuma fitaccen wurin ibada da ake kira Golden Temple, wuri mai matuƙar mihimmanci ga mabiya addinin Sikh.

Mutane da dama sun ɗauki wurin bautar a matsayin wurin da ke taimaka wa al'umma da abinci.

Wani fitattacen malamin adinin Sikh ne ya samar da birnin wanda ke yankin Punjab inda addinin Sikh ya samo asali a ƙarni na 16.

Addinin Sikh na da al'adar 'Seva', wato yi wa mutane taimako, ba tare da sa ran samun wata riba daga waɗanda aka taimakawan ba.

Mabiya addinin Sikh a duka faɗin duniya kan gudanar da 'Seva' a wuraren bautarsu, mafi yawan taimakon da suke yi wa mutane suna hadar da shara da ciyar da mutane abinci.

A gefe guda mabiya adinin na Sikh kan gabatar da 'Seva' a ƙashin kansu ta hanyar taimako da sadaukarwa.

A watan Afrilun 2021 lokacin da annobar Corona ta tarwatsa iyalai da dama a Indiya, mabiya addinin Sikh sun yi ta bayar da taimakon tukunyar iskar shaƙa da magunguna ga waɗanda ke cikin tsananin buƙata.

A lokacin kullen corona, mabiya addinin sun sadaukar da rayuwarsu wajen ciyar da abinci ga dubban likitoci a kowacce rana a Ingila.

Haka kuma a wasu biranen Amurka sun yi ta dafa abinci suna rabarwa kyauta.

Haka kuma a lokatun da ake buƙatar taimakon gaggawa, mabiya addinin kan taimaka musamman wajen ciyar da mutane abinci.

A birnin Amritsar, cibiyar mabiya addinin, batun 'seva' na daukar wani sabon salo, inda ake ciyar da duka mazauna birnin da ke buƙata abinci.

Domin kuwa babu wani mutum da ke kwana da yunwa a birnin, domin kuwa a koyaushe akwai abinci a wurin bautar da ke jiran duk mutumin da ke jin yunwa.

Ɗakin girkin wurin bautar, shi ne babban wurin dafa abinci, da ke iya dafa abincin mutum 100,000 a kowacce rana.

Ana maraba da masu buƙatar cin abincin daga kowanne ɓangare ba tare da nuna wariya ba, matuƙar suna buƙatar abinci da masauki, kuma a kowanne lokaci mutum ya je wurin ibadar ba zai rasa abinci ba.

Masu bukatar cin abinci ciki har da maza da mata da yara da manya, kan zauna a ƙasa cikin ƙaton ɗakin cin abinci da ke iya ɗaukar mutum 200 a lokaci guda domin cin abincin.

Yayin da wasu ke neman a ƙara musu bayan sun cinye abincin da ke gabansu, wasu kuwa sauri suke su gama cinye abincinsu domin ficewa daga ɗakin.

Mintuna 15 bayan gama cin abincin masu shara kan goge ɗakin, tare da sake gyara shi ga wasu mutane da za su sake shiga domin cin abincin.

Haka za a yi ta yi har tsawon sa'ao'i 24 na kowacce rana.

Hakan ya sa mutane da dama ke ziyartar wajen bautar a kowacce rana domin samun abinci daga taimakaon da ake yi a wurin.

A matsayinsa na birni na biyu mafi girma a yankin Punjab, Amritsar ya kasance wurin taruwar masu zanga-zanga a lokacin turawan mulkin mallaka.

Source: BBC