BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Garin da matasa ke guduwa su bar tsofaffi a India

Tutar Indiya da na amurka

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

Yayin da india ta zarce China a matsayin ƙasar da tafi yawan al’umma a duniya, akwai rikice-rikice a wasu bangarori na ƙasar inda ake fuskantar ƙarancin haihuwa da za ta maye gurbin masu tafiya ciragi, wanda hakan ya bar garin babu kowa sai tsofaffi.

Ma’aikacin BBC Soutik Biswas ya je garin Kumbanad, wani ƙauye cikin jihar Kerala wanda yake fama da ƙarancin rashin matasa.

Cikin shekaru, Kerala wani gari ne da ke fuskantar matsala da ba a saba gani ba: ɗalibai sun yi ƙaranci kuma maalamai ne ke fita da kansu suna neman ɗaliban domin kai su makaranta. Wani lokacin suke biyan kuɗin makaratar daga aljihunsu.

Wata makarantar firaimari da ta kai shekara 150 – wadda yara kan kai shekara 14 suna zuwa a Kumbanad tana da ɗalibai 50, wadda a baya na da ɗalibai 700 kafin ƙarshen shekarun 1980.

Mafi yawan ɗaliban ‘ya’yan talakawa ne da suke zama a gefen birnin. Yanzu tana da ɗalibai bakwai ne kawai, kuma babban ajinta na bakwai yana da ɗalibi ɗaya ne a 2016.

Samun ɗaliban da suka isa wani ƙalubale ne ga makarantar. Ko wanne ɗaya dag cikin malamanta na cire rupee 2,800 ne duk wata, daidai da dala 34 domin biyawa daliban makarantar kudin babur din da ke kai su da komar da su makaranta. Kuma suna zuwa gida-gida domin samun ɗalibai. Kuma ko makarantu masu zaman kansu a yankin haka suke aika malamansu domin samo dalibai, wacce ta fi ko wacce girma ita ce ke da ɗalibai 70.

A wani yammaci mai zafi a cikin makarantar, da wuya kaji karatu ko hayaniyar ɗalibai a makarantar. Maimakon haka malaman na koyar da yara ne da basu kai sun kawo ba, ajujuwan shiru.

“Ya zamu yi? Babu yara a garin. Ina nufin da wuya ka ga mutanen da ke zaune a nan,” in ji Jayadevi shugabar makarantar.

Daidai ta faɗa. Kumbanad shi ne tsakiyar lardin Pathanamthitta da ke Kerala inda yawan al’umma ke raguwa kullum ga rashin matasa. Wannan na faruwa ne a ƙasar da kashi 47 cikin dari na mutanenta ‘yan ƙasa da shekara 25 ne, kuma da yawansu an haife su bayan India ta ‘yantar da tattalin arzikinta a farkon shekarun 1990.

Wani asibiti na gwamnati da kuma wasu cibiyoyin gwajin marasa lafiya guda 30 da gidajen kula da tsofaffi uku – wata manuniya ce kan yadda tsaofaffi suka fi yawa a yankin.

Sama da bankuna 24 – cikin har da rassa takwas da ke kusa ƙasa da rabin kilomita – sun shiga tsarin da za a rika aiko musu kudi daga waje zuwa wajen iyalansu daga ko ina a faɗin duniya. Kimanin kashi 10 cikin dala biliyan 100 da aka aiko cikin Inda a bara an tura su ne jihar ta Kerala.

Kerala da makwabciyarta Tamil Nadu – suna gefen India ne – Tana kuma cikin jihohin da aka samu raguwar mutane inda ya kai kashi 4.9 tsakin sauran jihohin ƙasar, idan aka kwatanta da kidayar da aka yi a shekarar 2001 zuwa 2011. Yaron da aka haifa a jihar zai iya tsayin rai zuwa shekara 75 maimakon 69 adadin tsayin ran mafi yawan mutane a India.

Ywan haihuwar da ake yi ya yi ƙaranci ta yadda ba za a iya maye gurbin mutanen da suke fita ba – sama da shekara 30 kenan yanzu. Iyalan da ba su da yawa suna tabbatarwa da kowa ya samu ilimin da ya dace. Wannan ya janyo tserewar da matasa ke yi cikin gaggawa da sun fara girma daga ciki da wajen ƙasar domin samun damar rayuwa mai kyau, su kyale iyayensu su ka ɗai a gida.

“Ilimi ke sanya yara su samu kwarin gwiwar neman aiki da rayuwa mai kyau, don haka suke guduwa,” in ji Farfesa KS James da ke cibiyar kidaya a Mumbai.

Cikin wani jan gida da aka zagaye da ƙarafa a kauyen Kumbanad wata dattijuwa ce yar shekara 74 da ake kira Annamma Jacob,ta daɗe tana zaune ita kaɗai.

Mijinta bakanike ne da ya yi aiki da kamfanin mai na jihar, ya mutu ne a mutu ne a shekarun 1980. Sama da shekara 20 ɗanta ɗan shekara 50 ke aiki a Abu Dhabi kuma a can yake zaune. ‘Yarta na zaune ne kilomitoci kaɗan, amma mijinta na aiki ne a matsayin injiniya a Dubai sama da shekara 30.

Gidan da ke kusa da ita babu kowa ciki, a kulle yake, ‘yar mai gidan ce ta zo ta kwashe iyayenta suka tafi Bahrain, inda a nan take aiki a matsayin malamar jinya, ɗayan gidan kuma sun koma Dubai sun bai wa wasu tsoffi hayar gidansu.

Nesa kaɗan wani mutum ne da ake kira Chacko Mammen, wanda ke fama da ciwon zuciya da kuma ciwon siga, yana aiki a wata gona sa’o’i hudu a kullum, yana shuka ayaba. Mai shekara 64 ya yi aiki a Oman sama da shekara 30 a matsayin mai sayar da kayar kafin ya koma gida. Ya rufe ɗan kasuwancin da yake yi ya koma gida ne saboda ya gaza samun mutanen da za su tallafa masa. Yanzu bayan aiki tuƙuru yana iya sayar da ayabar kilogiram 10 a ranar daga gonarsa a kullum. “ Ba zan iya ɗaukar mai aiki ba,”

Rashin samun taimako wajen aiki ga a kauyen da babu matasa kullum abu ne mai wuya. Ko ‘yan ciranin da ke shiga jihar daga wasu jihohin ba kullum suke aiki ba, sau dayawa saboda rashin yarda da mutanen ƙetare, Kamar yadda Ms Jacob ta ce ita ba ta son ɗaukar hayar ‘yancirani.

Ni kaɗai nake rayuwa. Idan suka kashe ni fa?” In ji ta.

A ƙauyen da yake cike da tsofaffi da gidaje marasa yawa, ba a fiye aikata muggan laifuka ba.

‘Yan sanda sun ce ba a fiye yawan sata ba saboda mutane ba sa ajiye kudi, ko wasu abubuwa masu daraja a gida. Ba za su iya tuna lokacin da aka ce an kashe wani ba a yankin.

“Ko ina lafya. Mun fi samun ƙorafi kan zamba. Yan uwa ne ke zambatar tsofaffin ko masu taimaka musu ta yadda suke ɗaukar kudinsu a banki da sa hannunsu,” in ji Sajeesh Kuma babban sufeton yan sanda na yankin.

“Matsalarmu guda a nan tsofaffin mutane,” in ji mahaifin Thomas John wanda ke tafiyar da cibiyar kula da tsoffi a Kumbanad.

“Mafi yawan matasan na zaune a turai ne ba kuma da su da wani zabi sai dai su kai iyayensu wannan cibiya ta kula da tsofaffi,” in ji mahaifin John.

Ba da nisa ba, Dharmagiri mai shkara 75 a gefen wani gida mai dakuna 60 da tsofaffi, kuma dukkansu babu wanda ya haura shekara 60. A bara akwai sabbin mutane da aka kawi su 31.

Akwai gine-gine biyu, na maza daban na mata daban. Ana ƙasa samun yawan masu jiran samun ɗaki: ana sake gina wani ginin mai ɗaki 30 da zau ɗauki sama da tsofaffi 60.

“Da yawan matan da ke zaune nan an sha zambatarsu a baya. Wasu kuma ‘ya’yansu ko ‘yan uwansu ne suka yi watsi da su,” in ji mahaifin KS Mathews, wanda yake tafiyar da gidan.

Garin da tsofaffi suka cika shi, na fama da rashin ma’aikata da tserewar matasa wannan ke janyo raguwar al’umma a yankin, garuruwan da ke yankin na ƙara zama tamkar daji.

“Wannan shi ne abin da yake faruwa a duk inda ake samun ƙaurar mutane da dama. Kuma shi ne labarin iyalai da dama a cikin India,” in ji Farfesa James.

Source: BBC