BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Gasar cin Kofin Duniya ta Mata 2023: 'Yan Afirkan da za su kece raini

L-R: Ghizlane Chebbak, Refiloe Jane, Asisat Oshoala and Barbra Banda

Wed, 19 Jul 2023 Source: BBC

Za a fara Gasar cin Kofin Duniya ta mata ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, lokacin da ƙasashen Australia da New Zealand da ke karɓar baƙuncin haɗin gwiwa - za su buga wasanninsu na farko.

Afirka a karon farko za ta je gasar da ƙungiyoyin ƙasashe guda huɗu, bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta faɗaɗa gasar daga ƙasa 24 zuwa 32.

Najeriya, wadda ke bugu ƙirji da cin kofin Afirka tara, za ta bi sahun zakarun nahiyar na yanzu wato ƙasar Afrika ta Kudu, tare da Morocco da Zambia waɗanda za su yi bayyanar farko a gasar ta tsawon wata ɗaya.

Za a buga wasan ƙarshe ne a ranar 20 ga watan Agusta.

Gabanin irin wannan gasa wadda Afirka za ta tsallaka shingen karawar daf da kusa da ta ƙarshe, BBC Sport ta zaƙulo muku wasu zaƙaƙuran 'yan wasa huɗu da za su wakilci nahiyar.

Asisat Oshoala - Najeriya

Babu wata ƴar wasa da ta zarce Oshoala a fagen ƙwallon ƙafa na mata a Afirka - kuma ba a banza ta kai wannan mataki ba.

Bayan tumbatsar da ta yi a fagen duniya cikin 2014, lokacin da ta kasance mafi cin ƙwallo kuma 'yar wasa mafi fice a Gasar cin Kofin Duniya ta 'Yan ƙasa da shekara 20, tun daga sannan ne Oshoala ta shiga sahun manyan 'yan wasan ƙwallon ƙafa na nahiyar.

Ta lashe gasar cin kofin Afirka ta mata (Wafcon) har sau uku, kuma ta zama 'yar wasa mafi fice a biyu daga cikin gasannin, ta kuma zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya ta 2015 da ta 2019.

Idan ta zura ƙwallo a raga wannan karo, za ta zama 'yar Afirka ta farko da ta ci ƙwallo a gasannin cin kofin duniya na mata har sau uku, za kuma ta iya bunƙasa tarihinta na zama 'Yar Ƙwallon Afirka ta Shekara har karo shida.

Ƴar wasan ƙungiyar mata ta Barcelonan, ta je Gasar cin Kofin Duniya bayan ta buga ƙwallo a ƙungiyar tsawon shekara huɗu a jere inda ta zura ƙwallo 20 kuma cikin shekara biyu a jere ta zama 'yar wasa mafi cin ƙwallo tsawon shekara biyu a jere ga zakarun Turan na yanzu.

A ranar da ƙwallo ke yi da ita, 'yan wasan baya kaɗan ne za su iya gogawa da Oshoala, ganin yadda take iya cikakkiyar 'yar wasan gaba kuma ta mamaye fage da ƙarfin dannawarta da kuma gudun tsiya, amma takun kaifin basirar a kan ƙwallo da kuma wurin tsayawarta ne suka sanya ta fita daban da saura.

An cire ta daga gasar Wafcon ta bara ba, saboda rauni a gwiwa da ta ji a wasan farko, kuma ba ta samu damar buga wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai a watan Mayu ba, saboda raunin da ta ji a jijiyar ƙwauri lokacin wasan da Barca ta cinye ƙungiyar Wolfsburg, don haka 'yan Najeriya za su yi fatan ta zama cikin ƙoshin lafiya.

Barbra Banda - Zambia

Wata wadda ba ta samu damar zuwa gasar Wafcon ba, ita ce Banda, matashiya 'yar shekara 23, da ke da baiwar buga ƙwallo mafi ƙayatarwa a Afirka.

Ƴar wasan gaban ta bai wa duniya mamaki a shekarar 2021 lokacin da ta yi asin-da-asin wajen zura ƙwallo rigis ɗaya bayan ɗaya a gasar Olympics - ita ce ƴar ƙwallon da ta fara kafa wannan tarihi a tsawon shekarun da aka kwashe ana gasar - kafin a fitar da Zambia matakin wasannin rukuni.

Duk da haka, ƙwazon Banda ya kakare a bara lokacin da aka cire ta daga cikin 'yan ƙwallon da za su buga gasar Wafcon - a jajiberen gasar - bayan wata taƙaddama a kan jinsin da take wakilta.

Duk da wannan koma-baya, kyaftin Banda ta nuna gagarumar ƙwarewar shugabanci inda ta zauna a Morocco, ta yi jagorancin bayan fage ga ƙasarta, wadda ta ƙare gasar a matsayi na uku mai cike da tarihi.

Wani abin farin ciki ga Banda da kuma ƙasarta Zambia shi ne tun tuni aka amince ta koma fagen wasa, inda kuma ta dawo cike da razanarwa, ta hanyar cin ƙwallo goma a wasa biyar da ta buga yayin Cin Kofin Coasafa a watan Satumban bara.

A matsayinta na sabuwar zuwa, Zambia mai yiwuwa ne za ta buga salon wasan tsare gida da mayar da farmaki, kuma da Banda wadda masifaffen gudunta ke iya barin 'yan baya na ganin ƙura, suna da fitacciya a wannan harka ta tsere sa'a can a tsakiyar fili.

Bayan ƙulla ƙawance da Racheal Kundananji, wadda ta zura ƙwallo 25 a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta mata a ƙasar Sifaniya cikin kakar wasannin da ta wuce, su biyun suna iya zama ɗaya daga cikin 'yan wasa mafiya kai harin halakarwa a a Ostireliya da New Zealand.

Refiloe Jane - Afirka ta Kudu

Jane mai yiwuwa ita ce 'yar wasan da ba a cika yayata muhimmancinta ba a jerin 'yan ƙwallon nan, duk da kasancewarta mafi muhimmanci ga ƙasarta, a matsayinta na gajerar 'yar wasan tsakiya, tamkar ruhi cega ƙungiyar zakarun na Afirka.

Kasancewarta ginshiƙi ga irin ƙwallon da koci Desiree Ellis ke son ƙungiyar ta buga, Jane jigon raba ƙwallo ce ga Banyana Banyana.

Idan ta tsaya a gaban layin tsaron baya, tana da mayatacciyar ƙwarewa wajen gara ƙwallo ta je inda ta nufa, kuma tana iya kwantar da zafi-zafin wasa idan an tayar musu da hankali, hakan na ba da damar bunƙasa ga zalaƙar kai farmakin Afirka ta Kudu

Bayan ta yi bayyanar farko a wata karawar gasa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic cikin shekara ta 2012, Jane ta ci gaba da buga wa Afirka ta Kudu ƙwallo a duk wata babbar karawa, inda wasannin da ta buga suka kai 100.

A bara, likkafarta ta ƙara ɗagawa inda ta dinga riƙe muƙamin kyaftin ga ƙungiyarsu a matakin haɗin gwiwa, tare da ainihin daɗaɗɗiyar kyaftin ɗin Afirka ta Kudu Janine van Wyk - abin da ya kai ƙasar ga samun nasara a karon farko wajen ɗaukar gasar Wafcon bayan sun doke Morocco - sai dai a yanzu ita ce babbar kyaftin ɗin ƙungiyar saboda Van Wyk ta kwanta jinya.

Komawa Ostireliya, wani abu ne da ta saba, tun da a can ne, Jane ta fara sa hannu kan kwanturaginta na farko a matsayin ƙwararriyar 'yar ƙwallo da kulob ɗin Canberra United cikin shekara ta 2019 kafin ta koma ƙasar Italiya, inda yanzu take buga wa Sassuolo wasa (bayan zaman da ta yi a Milan).

Ko da yake, ba lallai ne ta iya cin ƙwallaye masu yawa ba ko kuma jaridu su buga wani labarin bajintarta, amma Jane za ta kasance ginshiƙi ga burin Afirka ta Kudu yayin da suke buga wannan gasa a karo na biyu..

Ghizlane Chebbak - Morocco

Duk da yake, Afirka ta Kudu da Najeriya sun fi ɗaukar hankulan 'yan jarida a gasar Wafcon ta bara, sai dai masu masaukin baƙin sun bai wa duniya mamaki lokacin da suka kai karawar ƙarshensu ta farko - da Ghizlane Chebbak a matsayin tauraruwa mafi haskakawa.

'Yar tsohon ɗan ƙwallon duniya Larbi Chebbak, wanda ya taɓa lashe Gasar cin Kofin Afirka a 1976, Ghizlane ta jagoranci ƙungiyar Atlas Lionesses matsayin kyaftin a zuwansu na farko gasar cin kofin Afirka ta mata a cikin shekara 20, bajintar da ta kai su ga samun cancantar Gasar cin Kofin Duniya ta farko.

Jagorantar ƙungiyar ƙasarta a gaba, Chebbak ta kammala gasar Wafcon a matsayin 'yar wasa mafi cin ƙwallo ta haɗin gwiwa, sannan gwarzuwar 'yar ƙwallo a gasar.

Duk da kasancewarta 'yar wasan tsakiya, Chebbak tun fil'azal ita mai cin ƙwallo ce. Tuni dai ta kafa tarihin zama wadda ta fi cin ƙwallo a Maroko, kuma a kwanan nan ta zamo 'yar wasa mafi fice wajen cin ƙwallo tsawon kakar wasa biyar a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, inda ta lashe gasar karo goma a jere da kulob ɗin AS FAR.

A watan Nuwamba, ta jagoranci ƙungiyar AS FAR wajen ɗaukar Gasar Zakarun Afirka a karon farko, sa'ar da suka doke mai riƙe da kofin Mamelodi Sundowns a wasan ƙarshe.

Chebbak kuma gwanar ban mamaki ce wajen sake dasa ƙwallo, kuma ko wajen buga firikik ko kwana ko kuma fanareti, da wuya ta ɓaras maka da ƙwallo, wani abu da mai yiwuwa zai kasance mai matuƙar amfani ga ƙungiyar da ta je gasar cin kofin duniya a karon farko.

Chebbak wadda akasari take sanya lamba 10 a a tsarar 'yan wasan tsakiya uku, ita ce kuma jigon ƙirƙiro salon wasa ga Atlas Lionesses, inda komai yake wucewa ta hannunta.

Ko da yake, ba lallai ne tana da matsanancin gudu ba, amma fasaharta da kaifin tunaninta wajen yanke shawara sun sanya ta zama tauraruwa.

Source: BBC