Super Falcons ta yi canjaras da Jamhuriyar Ireland a wasa na uku
Nigeriya ta sami kai wa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya ta mata da ake gudanarwa a Australiya da New Zealand.
Super Falcons ta yi canjaras da Jamhuriyar Ireland a wasa na uku a rukuni na biyu ranar Litinin.
Hakan na nufin Najeriaya ta kasance ta biyu a rukuni na hudu,bayan da ta hada maki biyar, yayin da mai masaukin baki Australiya ta ja ragamar rukunin da maki 6 bayan ta doke kanada da ci 4 - 0.
Najeriya ta kammala wasannin rukunin ba tare da an doke ta ba, wadda ta tashi ba ci da Canada da cin Australia 3-2 da canjaras da Ireland.
Yanzu Najeriya za ta kara da kasar da ta ja ragamar rukuni na hudu, wacce kan iya zama Ingila ko Denmark ko China a zagaye na biyu.
A sauran wasannin da aka buga a ranan Litinin Zambiya ta doke Costa Rica 3-1 a inda Japan da casa Sifaniya 4-0.
Za a fara buga wasannin zagaye na biyu a ranar 5 ga watan Agusta.