Kyaftin din Australia Sam Kerr
Kyaftin din Australia Sam Kerr ba za ta buga wasanni biyu na farko na gasar cin kofin duniya ta mata ba sakamakon raunin da ta samu a yayin da take atisaye.
Kerr ba za ta buga wasan farko na rukunin B na masu masaukin bakin da Jamhuriyar Ireland a filin wasa na Australia ba ranar Alhamis.
'Yar wasan mai shekaru 29, wadda ta fi kowa zura kwallaye a tarihin kasar Australia, ba za ta kuma buga wasa da Najeriya ba a ranar 27 ga watan Yuli.
Kerr yanzu za ta yi fatan samun lafiya a wasan karshe na Australia a rukunin B, da Canada ranar 31 ga Yuli.
'Yar wasan gaban Chelsea ta wallafa a shafinta na Instagram cewa ba karamin abin takaici ba ne raunin da ta samu.
Kerr ba ta nuna alamun rauni ba lokacin da ta yi magana a taron manema labarai da yammacin Laraba a filin wasan na Stadium Australia, wanda ya zo bayan atisayen karshe na kungiyarta kafin wasansu na farko.