BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ghana ta zama ta farko a duniya da ta amince da sabon riga-kafin maleriya

Anopheles Mosquito Africa12 Zazzabin cizon sauro na kashe kusan mutane dubu 620 a duk shekara, galibi yara

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Ghana ta zama kasa ta farko da ta amince a yi amfani da wani sabon riga-kafin zazzabin cizon sauro da masana kimiyyar da suka kirkiro shi suka bayyana shi a matsayin wanda zai haifar da gagarumin sauyi wajen yaki da cutar a duniya.

Riga-kafin mai suna R21 -yana aiki sosai sabanin wasu da aka kirkiro aka jarraba a baya a yaki da cutar ta maleriya.

Hukumar da ke sa ido kan magunguna ta Ghana ta yi nazarin bayanan da aka samu na gwajin karshe na ruwan maganin, kan rashin hadarinsa da kuma tasirinsa, wanda kuma ba ta bayyana ba, amma ta amince a yi amfani da maganin.

Ita ma hukumar lafiya ta duniya, WHO, tana duba yuwuwar amincewa da maganin.

Malaria tana hallaka kusan mutum dubu 620 a duk shekara yawanci kananan yara.

Masana kimiyya sun dauki kusan shekara dari daya suna fafutukar samar da maganin riga kafin da zai kare mutane daga cutar da sauro ke yadawa.

Gwajin da aka yi a Burkina Faso na sabon maganin na R21 ya nuna cewa yana tasiri kashi 80 cikin dari idan aka bai wa mutum shi kashi uku a tashin farko, sannan kuma bayan shekara a yi masa na karin karfafa aikinsa.

Sai dai ana ganin kafin a kai ga amincewa da yin amfani da maganin a kasashe da dama sai na ga yadda sakamakon gwajinsa ya kasance a kan wasu yara dubu biyar.

An sa ran za a kammala tare da bayyana sakamakon wannan gwaji a karshen shekarar da ta wuce, 2022 to amma har yanzu ba a wallafa sakamakon ba a hukumance.

Duk da cewa wasu gwamnatocin kasashen Afirka da masana kimiyya sun samu sakamakon a hannunsu.

Wakilin BBC ya ce bai ga sakamakon na karshe ba amma ya ce an gaya masa cewa sakamakon ya kasance kusan iri daya da gwaje-gwajen da aka yi a baya.

Darektan Cibiyar Jenner (Jenner Institute) a Jami’ar Oxford, inda aka kirkiro maganin Farfesa Adrian Hill ya ce, kasashen Afrika sun ayyana cewa: "za mu yanke shawara", bayan da aka bar mu a baya wajen raba riga-kafin cutar Covid-19 lokacin annobar korona.

Wakilin na BBC y ace, darektan ya gaya masa cewa: "Muna sa ran R21 ya yi matukar tasiri wajen rage mace-macen sa malaria ke haddasawa a yara a shekaru masu zuwa, kuma a nan gaba zai taimaka wajen kawar da cutar gaba daya."

Hukumar kula da inganin magunguna da kayan abinci ta Ghana wadda ta ga sakamakon ta amince a yi amfani da riga-kafin a kan yara ‘yan wata biyar zuwa shekara uku.

Wasu kasashen Afirka ma hadi da Hukumar Lafiya ta Duniya suna nazarin maganin.

Cibiyar Serum Institute ta India na shirin samar da kwalaben maganin tsakanin miliyan

100-200 a duk shekara, inda kuma za a kafa ma’aikatar da za a rika yin maganin a Accra, Ghana.

Ana sa ran kudin maganin na R21 ya kasance ‘yan daloli kawai.

Babban jami’in cibiyar ta Serum Adar Poonawalla,ya ce: "Kirkiro maganin da za iyi gagarumin tasiri a kan wannan cuta mai illar gaske ba karamin aiki ba ne mai wuyar gaske."

Ya kara da cewa kasancewar Ghana a matsayin kasa ta farko da ta amince da maganin wannan ba karamin cigaba ba ne a kokarinsu na yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro a fadin duniya.

Source: BBC