Menu

Guardiola ya lashe kofin UEFA Super Cup karo na uku

Guardiola tare da Erling Haaland

Thu, 17 Aug 2023 Source: BBC

Manchester City ta lashe kofin Uefa Super Cup a wasan da ake bugawa tsakanin wanda ya ɗauki kofin Zakarun Turai na Champions League da kofin Europa League.

Man City ta samu nasarar doke Sevilla 5-4 a bugun fenariti a Athens, bayan wasan ya kare 1-1.

Kungiyar Pep Guardiola ta sha kashi a hannun Arsenal a bugun daga kai sai mai tsaron gida a lokacin da suka kara a wasan Community Shield amma wannan karon lamari ya canza lokacin da dan wasan Sevilla Nemanja Gudelj ya zubar wa Sevilla da bugunta ta karshe.

Youssef En-Nesyri ne ya fara zura kwallo a ragar City a minti na 25 kafin Cole Palmer ya farke wa zakarun Ingila a minti na 63.

Guardiola ya bayyana yadda yake matuƙar son lashe kofin - kuma murnar da ya yi a lokacin da aka tashi bugun daga kai sai mai tsaron gida ya bayyana hakan.

Bayan nasarar da ya yi a baya tare da Barcelona da Bayern Munich, ya zama koci na farko da ya lashe gasar tare da kungiyoyi daban-daban guda uku.

Source: BBC