BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Gundogan zai tafi Bercelona a ƙarshen wata

Ilkay Gundogan

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Kaftin ɗin Manchester City Ilkay Gundogan zai koma ƙungiyar Barcelona, inda shi ne zai daidaita da sabon kulob ɗin nasa bayan ƙarewar kwanturaginsa a ƙarshen wannan wata.

Man City ta yi wa Gundogan mai shekara 32 sabon tayin kwanturagi amma ana jin cewa ya daidaita a kan wata yarjejeniya da ta fi tsoka tsa tsawon shekara uku da zakarun na ƙasar Sifaniya.

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana alla-alla ya ci gaba da aiki tare da Gundogan, wanda jigo ne a nasarar ɗaukan kofina uku da kulob ɗin a wannan kaka.

Bajamushen ɗan wasan tsakiyar ya buga wasa 51 a kakar wasanni ta 2022 - 23, inda ya ci ƙwallo 11.

Source: BBC