Menu

Gwamnatin Neja ta ce Boko Haram ta kafa tuta wasu yankunan jihar

 118218732 B41174a3 Acad 44d3 88df 36750d980213 Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello

Tue, 27 Apr 2021 Source: BBC

Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta ce ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar ya ce mayaƙan sun kafa tuta ne a ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro, kamar yadda babban mai ba shi shawara kan watsa labarai Mu'awuya Muye ya fitar da sanarwa.

"Sun kwace yankin sun kuma kafa tutarsu, ina tabbatar da hakan a yanzu," in ji gwamnan.

Ya ce abin da ya daɗe yana nuna wa gwamnatin Tarayya ga shi nan yanzu yana faruwa.

A cewar Gwamnan "Abin takaici har ya kai wannan matakin kuma idan ba a yi hankali ba, Abuja ba za ta zauna lafiya ba."

Gwamnan ya kuma bayyana damuwa kan yadda a cewarsa mayaƙan na Boko Haram ke kwace matan mutane da ƙarfi. Kuma suna son mayar da yankin a matsayin gidansu kamar yadda suka yi a dajin Sambisa.

Ya ce duk da cewa bai yanke kauna a kan Gwamnatin Tarayya ba, ba zai ƙara jira ba, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ga dalilan da za su sa a ɗauki matakin soja.

Sanarwar kuma ta ce ƴan bindiga na kwarara ne daga ƙauyen Kupana na jihar Kaduna inda suke satar mutane tare da yi wa mata fyade.

Source: BBC
Related Articles: