BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Gwamnatin Serbia na neman bijire wa yarjejeniyar zaman lafiya da Musulmi

Hoton alama

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

'Yan majalisar dokokin Bosnia and Herzegovina, Sabiyawa masu rinjaye sun kada kuri'ar bijire wa duk wani hukunci da kotun tsarin mulkin kasar za ta yi.

Matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar da kuma yarjejeniyar zaman lafiya ta 1995 ( Dayton Peace Agreement), wadda ta kawo karshen yakin Bosnia.

Ita dai kotun tsarin mulkin da 'yan majalisar suka kada kuri'ar bijire wa tana daya daga cikin muhimman hukumomin kasar.

Ba ya ga kare kundin tsarin mulkin kasar, kotun tana kuma iya yin hukuncin da zai kawar da na duk wata kotu a kasar, wanda hakan na nufin hatta dokoki da gwamnatocin yanki suka yi.

Wannan matsayi na kotun ne ya sa babban dan siyasar kabilar Sabiyawa, kuma jagoran gwamnatin yankin, Milorad Dodik yake hari da kokarin ganin bayan kotun.

Tun a baya kafin a zo wannan matakin ya yi yunkurin yi wa kotun kafar ungulu, ta hanyar kin zabar alkalai 'yan kabilar Sabiya da za su kasance a cikinta.

Da ya ga hakan bai yi aiki ba sai ya bullo da wannan doka a yanzu wadda yankin zai ki martaba hukuncin kotun.

Wannan ne ma ya sa har ofishin jakadancin Amurka a babban birnin kasar Sarajevo, ya ya mayar da martani kan matakin inda ya bayyana shi da cewa hari ne na rashin tunani da sakarci ga yarjejeniyar zaman lafiya ta 1995 wato Daytone Peace Agreement".

Haka kuma ofishin jakadancin Amurkar ya nuna cewa yankin shi kadai ba zai iya zartar da wannan doka da za ta soke hukuncin kotun tsarin mulkin kasar ba.

Shi dai Mista Dodik ya dade yana hankoron ganin gwamnatin Serbia ta ware daga gwamnatin tarayya ta Bosnia.

Sakamakon yakin da aka dauki tsawon lokaci ana yi a shekarun 1990, aka raba Bosnia biyu, zuwa yankuna masu cin gashin kansu, wato Jamhuriyar Sabiya da kuma yankin gwamnatin hadakar Musulmi da 'yan kabilar Crotia, inda gwamnatin tarayyar mai rauni take rike da su a sama.

Source: BBC