BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Gwamnatin Syria ta bayar da damar kai agaji yankin 'yan tawaye

Hoton alama

Fri, 14 Jul 2023 Source: BBC

Gwamnatin Syria ta sanar da cewa za ta bar Majalisar Dinkin Duniya ta kai kayan agaji ga yankunan da ke hannun ‘yan tawaye a arewa maso yammacin kasar, ta hanyar mashigar Bab al-Hawa wajen iyaka da Turkiya, tsawon wata shida.

Kwamitin tsaro na majalisar ya bayar da umarnin gudanar da aikin har zuwa ranar Litinin.

Amma kuma mambobin Kwamitin sun ki sabunta shirin, inda Rasha wadda kawace ga Syria ta yi amfani da ikonta na kujerar na-ki ta hana sabunta aikin tsawon wata tara.

Haka ita ma kuma daftarin da ta gabatar na tsawaita aikin da wata shida bai samu kuri’un da yake bukata ba kafin ya samu karbuwa.

A lokacin da yake bayar da wannan sanarwa jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya, Bassam Sabbagh, ya gaya wa manema labarai cewa gwamnatinsa ta bai wa majalisar izinin ci gaba da kai kayan agajin ta kan iyaka, matukar majalisar za ta yi wannan aiki da sharadin da gwamnatin Syria ta gindaya na tsara aikin tare;

Ya ce: ‘’Gwamnatin Jamhuriyar Larabawa ta Syria ta dauki wannan mataki na koli ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya da hukumominta na musamman damar amfani da mashigar Bab-al-Hawa domin kai kayan tallafi ga fararen hula da ke cikin bukata a arewa maso yammacin Syria, da cikakken hadin kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Syria tsawon wata shida, farawa daga ranar 13 ga watan Yuli, 2023.’’

Da take mayar da martani dangane da wannan labari Jakadiyar Birtaniya a Majalisar ta Dinkin Duniya , Dame Barbara Woodward, ta ce yin wannan aiki ba tare da sa idon Majalisar Dinkin Duniya ba, tamkar bayar da ikon wannan muhimmin aiki ne ga mutumin da ya jefa al’ummar Syria cikin akuba.

Ta ce Birtaniya ba za ta saurara ko wani jinkiri wajen sake gabatar da wannan batu ga kwamitin tsaron ba

Sai dai kawar Syria a kwamitin tsaron, wato Rasha ta dade tana cewa aikin kai kayan tallafin na Majalisar Dinkin Duniya, wanda za a bi ta iyaka, ke da haddin ‘yancin Syria ne.

Kuma tun a shekarun baya a lokacin tattaunawar da ak rika kai ruwa rana a kanta, an rage yawan hanyoyin da za a rika bi wajen kai agajin daga hanyoyi hudu zuwa daya kawai, ta hanyar Bab Al- Hawa.

Yanzu duk wani kayan agaji da za a kai yankin arewa maso yammacin kasar ta Syria, yankin da ke hannun ‘yan tawaye ya dogara ne ga amincewar gwamnatin Syriar, kuma a kowa ne lokaci za ta iya hana wa.

Haka kuma yanzu wannan amincewa da kwamitin tsaron ya yi ta kai kayan agajin ta wannan hanya daya tilo ta Bab-al-Hawa a wannan karon ma, wadda hanya ce ta kan iyaka, za ta kare ne a ranar Litinin, bayan da Rasha ta hau kujerar na-ki a kan sabunta ta, da cewa ta saba wa ’yancin Syria.

Source: BBC