Wasu dalibai 'yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan sakamakon yakin da ake yi a can, sun sake kira ga gwamnatin Najeriya ta taimaka ta dawo da su gida.
Sun koka inda suka ce suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin sanin makomarsu, sannan wurin da aka ba su duke fakewa ma an koresu bayan cikar wa'adin da aka dibar musu.
Daya daga cikinsu da bai so a ambaci sunan shi ba, ya shaidawa BBC cewa su na cikin halin, ''Innalillahi wa inna Ilaihirraji'un, sakamakon mun samu matsala a inda muke, sojojin da muke tare da su sun yi yunkurin kisan daya daga cikinsu bayan samu wata matsala, kan an ba mu wa'adin tashi daga wurin amma ba mu tashin ba.
Mun shigar da korafi ofishin jakadancin Najeriya amma ba su ce mana komai ba, a karshe dai an kore mu akan titi mu ke tare da kayanmu,'' inji shi.
Ya ce tun da fari, ofishin jakadancin Najeriya ne ya nema musu alfarmar zama a jami'ar Al-Qur'ani da ke jihar Port Sudan, a lokacin da ake kwashe dalibai 'yan Najeriya watanni kusan 9 da suka gabata, kuma an jima ana musu kora da hali.
''Mu na da matsaloli da dama, babu abinci ko wurin kwanciya, babu ruwan sha mai tsafta. A baya wasu kungiyoyi masu zaman kan su na kasar Qatar da Majalisar Dinkin Duniya su na taimaka ma na da ruwa amma daga baya mazauna yankin sun hana su.
A yanzu haka an kai watanni biyar ofishin jakadancin Najeriya a Sudan bai tuntube mu ba, babu abin da suka taimaka ma na da shi. Wasu daga cikin dalibai ma an kama su kan zargin aikata wasu laifuka sakamakon yakin da ake yi a Sdan, su na can gidan yari a kulle.''
Sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta waiwaye su domin dawo da su gida, saboda sun kasa samun hanya ta kasa da za su tsallako su dawo gida.
A watan Afirilun 2023 ne yaƙi ya barke a kasar ta Sudan, tsakanin sojojin gwamnatin Janar Abdel Fatta al-Burhan, da na rundunar RSF da Janar Muhammad Hamdan Dagalo da ake kira Hemeti ke jagoranta.
Dubun-dubatar farar hula sun rasa muhallansu, abin da ya sanya su yin gudun hijira a ciki da wajen Sudan kamar kasashen Tchadi da Sudan ta Kudu.
Tun daga lokacin kasashe da dama suka fara kwashe 'yan kasarsu da dalibai da ke karatu a can, Najeriya ma ta bi sahun hakan bayan daukar lokaci aka kwan-gaba-kwan-baya kan lamarin.
Sai dai da alama har yanzu, tsugune ba ta kare ba kan batun dalibai da ma 'yan Najeriyar da ke cikin halin ni 'ya su a can.
A daidai lokacin da yakin ke kara kazancewa, ya yin da bangarorin biyu ke kara dannawa da karbe ikon wasu jihohin Sudan ciki har da jihar Jazeera a baya-bayan nan.