Gwamnatin tarayya ta shawarci jihohin ƙasar su yi cikakken amfani da gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Najeriya a baya-bayan nan, don kyautata rayuwar fursunoni a gidajen yari.
Wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gida, ta ambato Minista Rauf Aregbesola na cewa daga ƙarshen watan Disamban bana, gwamnatin tarayya za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasar.
Ya ce idan gwamnatocin jihohi suka fara amfani da tsarin mulkin da aka yi wa gyaran fuska, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba wa hannu, hakan zai taimaka wajen ƙara rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya.
Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu.
Ya nanata buƙatar yin cikakken garambawul ga tsarin shari'ar laifuka wanda ya ce zai taimaka wajen rage alƙaluman tayar da hankali na mutanen da ke jiran shari'a a gidajen yari.
Sanarwar ta ambato ministan na cewa "Muna fatan gwamnatocin jihohi za su ci gajiyar tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa gyaran fuska, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai kwanan nan, abin da ya mayar da harkar kula da gidajen yari zuwa sashen ayyukan haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.
Ya ce abu ne mai muhimmanci idan gwamnatocin jihohi za su fara zuba kuɗi cikin harkokin kula da gidajen yari".
Ministan ya kuma ce, "Abu mafi muhimmanci shi ne buƙatar yi wa tsarin shari'ar laifuka garambawul.
Na sha yin wannan magana, kuma zan ci gaba da yin ta, cewa kashi 70 na mutanen da ake tsare da su a gidajen yari, suna zaman jiran shari'a ne".
A cewarsa, wani abin takaici game da haka, shi ne "bisa doka ba za mu iya fara ƙoƙarin gyaran halayensu ba, saboda ana ɗaukar su ne a matsayin marasa laifi, sai dai waɗanda bisa raɗin kansu suka zaɓi shiga".
"Da yawansu sun shafe tsawon lokaci fiye ma da zaman hukunci na laifin da ake zargin sun aikata," Aregbesola ya ce.
Hakan, in ji shi yana sanya su nuna halayyar neman tashin hankali kuma su ne babban ƙalubale ga sha'anin tabbatar da ɗa'a da ikon kula da cibiyoyin tsare mutane a Najeriya.
Ya ce kamata ya yi gwamnatocin jihohi, su yi garambawul ga tsarin gudanar da shari'o'insu, ta hanyar sanya iyaka a tsawon lokacin da ya kamata a kammala shari'a don tabbatar da yin shari'o'i cikin sauri.
Hakan a cewar ministan cikin gida, zai kawo ƙarshen dogon lokacin da ake kwashewa ana shari'a da kuma tsare mutane tsawon lokaci maras iyaka, a kan zargin aikata laifi da kuma rashin adalcin da ke tattare da haka.