Menu

Haaland ya kai Man City kwata fainal a Champions Leage

Erling Haaland

Tue, 14 Mar 2023 Source: BBC

Manchester City ta kai zagayen quarter finals a Champions League, bayan da ta doke RB Leipzig 7-0 a Etihad.

Erling Haaland ne ci mata kwallo biyar rigis a wasan, wanda ya fara cin ta farko a minti na 22 da fara wasa, sannan ya kara na biyu minti 22 tsakani.

Kwallo na 30 kenan da ya ci a Champions League a wasa 25, ya zama matashi mai shekara 22 da kwana 236 da ya ci kwallo 30 da wuri a gasar.

Daf da za a je hutu Haaland ya kara na uku, sannan Ilkay Gundogan ya kara na hudu minti hudu da komawa zagaye na biyu.

Haaland ya ci kwallo uku rigis a wasa sau biyar a City a bana a dukkan fafatawa, shine na farko a Premier da ya yi wannan bajintar bayan Harry Kane a 2016-17.

Daga baya Haaland ya kara biyu a raga, kenan biyar ya ci shi kadai a fafatawar.

Ya zama na uku da ya ci kwallo biyar a wasa daya a Champions League, bayan Luiz Adriano a Oktoban 2014 a wasa tsakanin Shakhtar Donetsk da BATE Borisov da Lionel Messi a Maris din 2012 tskanin Barcelona da Bayer Leverkusen.

Daf da za a tashi Kevin de Bruyne ya kara na bakwai a ragar RB Leipzig.

City ta kai zagayen gaba da kwallo 8-1, bayan da suka tashi 1-1 a wasan farko zagayen 'yan 16 a gasar zakarun Turai ranar 22 ga watan Fabrairu.

Wasa na hudu kenan da suka fafata a tsakaninsu a Champions League, inda City ta yi nasara a biyu da canjaras daya, leipzig ta ci daya.

Source: BBC