Menu

Halin da ake ciki bayan wawar abinci a jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Adamu Fintiri

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Al'umma na ci gaba da tsokaci a kan wawar kayan abincin da ta faru a Yola, babban birnin jihar Adamawa. Wasu dai na alaƙanta wawar da aka yi ranar Lahadi da halin matsin rayuwa da yunwar da ake fama da ita a sassan Najeriya.

Duk da haka, wasu suna cewa wawar dukiyar ba za ta taɓa zama hujja ba, saboda yin hakan tamkar sata ce.

Zuwa yanzu dai, hukumomi ba su ce ga yawan kayan abincin da aka wawashe daga rumbunan ajiyar ba.

Gungun matasa, maza da mata ne suka fasa wani rumbun ajiyar kaya da shagunan kasuwa, waɗanda ba na gwamnati ba a cikin yankin Jimeta, inda suka yi ta wawar buhu-buhu na abinci da sauran kayan da aka ajiye.

Gwamnatin jihar Adamawa ta sassauta dokar hana fita da ta sanya ranar Lahadi a faɗin jihar sa'o'i bayan ɓata-gari sun far wa rumbunan abincin tare da yin wawaso.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamna, Humwashi Wonosikou ya fitar, ta ce an sassauta dokar ne bayan zama da jami'an gwamnati da kuma shugabannin tsaro suka yi a safiyar Litinin wanda ya samu jagorancin mataimakiyar gwamnan, Farfesa Kaletapwa Farauta.

“An sassauta dokar inda yanzu za ta yi aiki daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma kuma za mu ci gaba da duba yanayin da al'amura suke. Jami'an tsaro kuma za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da ganin an bi dokar," in ji sanarwar.

Gwamnati ta kuma gargaɗi ɓata-gari da kuma jama'a cewa duk wanda ya saɓa wa dokar zai fuskanci hukunci.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar ta ce tana ci gaba da tattara alkaluman ɓarnar da ɓata-garin suka yi a rumbunan kayan abinci.

"Wawar na da nasaba da tsadar rayuwa"

Wani ɗan jarida daga Yola, fadar gwamnatin jihar ya tabbatar wa BBC cewa jami'an tsaro na ci gaba da shawagi domin tabbatar da ganin ɓata-gari ba su sake far wa rumbunan kayan abinci ba kamar yadda ya faru ranar Lahadi.

Ya ce auka wa rumbunan abincin na da nasaba da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta yi a baya-bayan nan cewa za a bai wa mutane agaji don rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur bayan wata ganawa da gwamnonin jihohi.

"Waɗannan matasa sun ɗauka cewa wannan karo ma an riga an ajiye kayan abinci a rumbunan gwamnati kamar yadda aka yi a lokacin korona, amma bayan zuwansu sai suka tarar da su a rufe."

Ɗan jaridar ya ce a kan hanyarsu ta komawa ne suka fara far wa rumbunan kayan ɗaiɗaikun mutane da kuma shagunan ƴan kasuwa domin wawason abinci.

Ya ce hakan ya faru ne saboda shiga cikin jama'a da ɓata-gari suka yi, inda suka fara kwasar dukiya kamar wayoyin salula da sauran kaya, abin da ya janyo gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa na sanya dokar hana fita domin shawo kan lamarin.

"Ɓarnar tana da girman gaske"

Wata ganau mai suna Hauwa'u Musa wadda gidanta yake kusa da rumbunan abincin da aka fasa, ta bayyana cewa tana zaune cikin gida kwatsam sai ta ga jama'a na ta ketarawa ta katangar gidanta suna wuce zuwa rumbun.

"Babu abin da za ka gani sai matasa da ke ta fito da buhunan abinci, idan ka ga gidana a yanzu, za ka ce yaƙi aka yi har ta kai ga sun ɓalla min ƙofar gida," in ji Hauwa'u.

Ta ce ɓarnar da aka yi tana da girma saboda buhunan masara da ta ga an fitar ba za su misaltu ba domin suna da yawa.

Ta ce lokacin da abin yake faruwa tsayawa ta yi ita ma domin tsare gidanta daga ɓata-gari.

Ta ƙara da cewa matasan sun yi amfani da wani abu kafin fasa rumbun saboda girmansa.

Hajiya Hauwa'u ta ce an ɗauki tsawon sa'a biyu ana wawar kayan abinci kafin jami'an tsaro su kai ɗauki, inda suka zo suka yi ta harbi cikin iska.

Me jama'ar gari ke cewa?

Tun bayan fasa rumbun adana abincin, mutane da dama a Yola, fadar jihar ta Adamawa na ta nuna ɓacin-rai kan abin da matasan suka yi.

Alhaji Lawan Smart, wani ɗan kasuwa ya yi tir da abin da ya faru saboda a cewarsa al'amarin zalunci ne ƙarara wanda ba sa fatan sake ganin ya faru.

Ɗan kasuwar ya ce ya kamata iyaye su kula da 'ya'yansu da janyo hankalinsu kan yadda za su guji aikata ba daidai ba.

"Dokar ta shafi kasuwancinmu, musamman ma mu ƙananan ƴan kasuwa wanda sai mun fito muke samun abin kai wa bakin salati, gaskiya an ci zarafinmu," in ji Lawan Smart.

Ya ce saka zai janyo nakasu ga ɓangaren kasuwancinsu saboda ba kowane mutum ne zai fito zuwa kasuwa ba a yanzu saboda ɗar-ɗar na abin da zai je ya dawo duk da cewa gwamnati ta sassauta dokar.

Source: BBC