Menu

Han Lay: Sarauniyar kyau da ke yaƙi da juyin mulkin Myanmar

 117799886 Mediaitem117799885 Sarauniyar kyau ta Myanmar, Han Lay

Wed, 7 Apr 2021 Source: BBC

Jawaban da sarauniyar kyau ta Myanmar, Han Lay, ta yi sun karade ko'ina tare da zama babban labari.

Amma a lokacin da Han Lay ta yi magana a makon da ya wuce kan zargin cin zarafin da ake yi wa sojojin kasar, sai bayanan na ta suka fara gwara kawuna.

"A yau a kasata Myanmar ... mutane da dama na mutuwa," ta fadi haka a wajen bikin sarauniyar kyau ta shekarar 2020 a kasar Thailand. "Don Allah ku taimaka wa Myanmar. A yanzu muna bukatar taimakon gaggawa daga kasashen waje."

A watan da ya gabata, Han Lay, 'yar shekara 22, tana daga cikin masu zanga-zangar kin jinin sojoji da aka yi a babban birnin Yangon kasar.

An fara zanga-zanga a Myanmar watanni biyu da suka wuce, lokacin da sojoji suka karbe iko da kasar tare da hambarar da zababbiyar shugaba Aung San Suu Kyi ta jam'iyyar National League for Democracy.

Lokacin da dubban mutane suka bazu a titunan kasar don zanga-zanga kan juyin mulkin da aka yi a kasar, sojoji sun mayar da martani ta hanyar fesawa masu zanga-zangar ruwa dan tarwatsa su. Mako guda bayan nan suka fara amfani da harsasan roba, daga bisani kuma harsashi mai kisa.

Mummunar rana cikin ranakun zanga-zangar ita ce Asabar din karshen mako, inda aka kashe sama da mutum 100.

Wata kungiya da ke sa ido kan halin da ake ciki ta ce wadanda aka kashe sun kai 500. Ita kuma kungiyar agaji ta Save the Children ta ce yara 43 na cikin wadanda aka kashe.

Han Lay, wadda ta karanci ilimin sanin dan Adam a jami'ar Yangon, ta yanke shawarar amfani da matsayinta wajen fadakarwa kan halin da kasarta ke ciki a duk inda ta je taro.

"Ana tsare 'yan jarida a Myanmar,... don haka na yanke shawarar yin magana," a cewarta yayin wata hira da BBC ta wayar tarho daga birnin Bangkok.

A yanzu ta damu matuka kan jawabin da ta yi na minti biyu, wanda ka iya sanya ta shiga baƙin littafin sojoji. Ta ce ta yanke shawarar zama aThailand na akalla wata uku.

Han Lay ta ce ta kafin tafiyarta Thailand ta san za ta sanya kan ta cikin hadari, sannan dole ta bar gida na wani lokaci.

"Na damu kan halin da 'yan uwana da masu tsaron lafiyata suke ciki saboda kalaman da na yi masu yawa kan sojoji da halin Myanmar. A Myanmar, kowa ya san inda ya kamata ya yi magana kan halin da kasar ke ciki," inji ta.

"Kawata ta fada min kar na koma Myanmar."

Fargabarta ba ta zamo ta karya ba. A makon da ya wuce jami'an tsaro sun fitar da warantin kama fitattun mutane 18 a kasar, ciki har da suka shahara a shafukan sada zumunta da 'yan jarida biyu, da ake zargi da karya doka da kuma shirin bata wa wasu sojoji suna,' kamar yadda kafar yada labaran kasar ta rawaito. Dukkan mutanen sun nuna rashin goyon baya kan juyin mulkin.

Han Lay ta ce kawo yanzu sojoji ba su tuntubeta ba, ko wani jami'i kan jawabin da ta yi, amma ta ce ana tura mata sakwannin batanci da barazana ta shafukan sada zumunta.

"Su na min barazana shafukan sada zumunta, su na cewa kurkuku na jira na da zarar na koma Myanma," inji Lay. S a kuma ta san wadanda suke tura ma ta sakwannin ba. Amma ta ce ta na samun goyon bayan masu bibiyar shafukan sada zumunta sosai.

An kulle yawancin kawayen Han Lay da suka shiga zanga-zanga a makon farko a kurkuku, kamar yadda ta shaidawa BBC. Mataimakin kungiyar fafutukar kubutar da fursunonin siyasa (APPP), ya ce sojoji sun kama mutane 2,500 da suka nuna kin amincewa da juyin mulkin.

Han Lay kuma ta ce an kashe daya daga cikin abokansu.

"Ba ma ya cikin zanga-zangar. Ya je da maraicen wata rana ne ya je kantin shan gahawa, kawai wani ya harbe shi," inji ta.

Iyalan Han Lay ba sa cikin wata barazana, sai dai ba a samunsu ta wayar salula sakamakon yadda ake yawan katse hanyar internet a Myanmar. Ta kuma roki BBC ka da a wallafa sunan garinsu, dan ba su kariya.

Jawaban da Han Lay ta yi a bainar jama'a, da suka hada da sukar sojojin Myanmar, da kiran magoya bayanta a shafinta su mara mata baya wajen akwo sauyi a kasatta, ba sabon abu ba ne ga masu mukami irin na ta.

A jawabin da ta yi gabannin fara bikin sarauniyar kyau, sarauniyar kyawu ta Cambodia, Lyv Chili, ta yi kira ga masoyanta sun tsame kan su daga shiga siyasa.

Amma Han Lay ta ce tana da hakkin yin magana. Ta ce Ms Suu Kyi ce ta bata kwarin gwiwa. A makon da ya wuce aka gurfanar da hambararriyar zababbiyar shugabar a gaban kotu kan take dokokin Myanmar da za a iya yanke mata zaman kason shekaru 14.

A baya-bayan nan Han Lay ta gama karbar horon zama mai kula da walwalar fasinja a cikin jirgi idan ta kammala karatu, amma yanzu ta ce ba ta san abin da ya kamata ta yi ba. Wasu kuma na kokarin ganin ta shiga siyasa, amma ta ce wannan ba bangaren ta ba ne.

Kawo yanzu ta yanke shawarar ci gaba da amfani da muryarta kan halin da Myanmar ke ciki.

"Wadannan laifukan take hakkin dan adam ne, dan haka muke son Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin gaggaw," inji Lay. "Mu an son a dawo mana da shugabanninmu, a dawo mana da dimukradiyya kasar mu."

Source: BBC