Menu

Hankalin duniya ya karkata ga laluben jirgin ruwan ƙarƙashin teku

Jirgin ruwan na sunduki da ke tafiya a karkashin teku

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Wannan aiki na neman jirgin ruwan na sunduki da ke tafiya a karkashin teku, wanda ke dauke da mutum biyar, ya dugunzuma hankalin duniya.

Musamman manyan kasashen Yamma, ganin cewa iskar shaka da jirgin ya yi guzuri wadda mutanen ke amfani da ita ta doshi karewa, wadda ta rage an yi kiyasi ba ta kai ta tsawon sa’a 20 ba, ga shi kuma har yanzu lalube kawai ake yi.

Jami’an tsaron gabar tekun Amurka da ke jagorantar wannan aiki, wanda ake ci gaba da tura duk wasu manyan na’urori masu fasaha ta yankan shakku da jirage na sama da na ruwa da na karkashin teku, sun ce an fadada yankin da ake tsammanin ganin jirgin ruwan a tekun na Atalantika saboda sauyin yanayi da kuma igiyar ruwa.

A yanzu an fadada laluben a yankin da ya ninka jihar Connecticut ta Amurka biyu, jihar mai fadin murabba’in kilomita sama da dubu goma sha uku, zuwa dubu 26 ke nan a yanzu, inda ake neman jirgin a sama da kuma cikin teku, zurfin kilomita hudu.

Jami’an sun ce ana jin karin kara a yankin da ake neman jirgin ruwan. Amma kuma sun ce ba su san karar ta meye ba, illa dai masu aikin ceto na ci gaba da duba wajen.

Kyaftin Jamie Frederick da ke jagorantar bayar da bayanai kan aikin ya bayyana kwarin gwiwarsu a kan aikin, inda ya ce har yanzu suna da fata za a ga jirgin a kuma ceto mutanen ciki:

Ya ce, ‘’ Ah, wannan aiki ne na nema da ceto, kashi dari bisa dari. Muna. Tsundum muke a tsakiyar aikin na nema da ceto, kuma za mu ci gaba da sanya duk wani abu da muke da shi a wannan kokari nagano jirgin na Titan da mutanen da ke cikinsa.’’

Jiragen sojin sama na Canada sun shiga aikin, sannan akwai jiragen ruwa da na’urori masu tafiya a ruwa da ka iya jiyo motsi ko kara, da daukar hotuna, wadanda butun-butumi masu fasaha ke sarrafawa duka an baza su a aikin a teku.

Ana sa ran samun wani cigaba da zai karfafa gwiwar gano jirgin ruwan da kuma ceto mutanen da ke ciki idan wani jirgin ruwa na Faransa da ke kan hanya ya isa wajen.

Jirgin na Faransa zai iya aika mutum-mutumi mai na’ura can cikin tekun, zurfin kafa dubu 20.

Mutane biyar da ke cikin jirgin ruwan na karkashin teku wanda ya bata tun ranar Lahadi da safe, a kan hanyarsa ta zuwa kasan tekun na Atalantika, inda katafaren jirgin ruwan nan na Titanic da ya yi hadari a shekarar 1912 yake, ‘yan Birtaniya ne uku Hamish Harding da attajiri Shahzada Dawood da dansa Suleman Dawood dalibi mai sheakara 19.

Sai mai ninkaya dan Faransa Paul Henri Nar-jo-lay da shugaban kamfanin jirgin ruwan na yawon bude idanu.

Source: BBC