Har yanzu tsohon ɗan ƙwallon Manchester United da Ingila, Jesse Lingard, na da damar buga wa West Ham wasa a kakar wasa ta bana yayin da yake ci gaba da yin atasaye tare da ƙungiyar.
A ƙarshen kakar wasa ta bara ne Lingard ya zama maras ƙungiya bayan ya bar Nottingham Forest.
Ranar Laraba da dare hukumar Premier League ta wallafa sunayen 'yan wasa 25 na kowace tawaga a gasar.
Sai dai, duk da cewa babu ƙungiyar da za ta iya sauya tawagarta, ƙungiyoyin za su iya ƙara yawan 'yan wasa idan ba su kai 25 ɗin ba.
West Ham 24 take da su zuwa yanzu, abin da ke nufin har yanzu Lingard zai iya buga mata wasa. Ƙungiyar ɗaya ce daga cikin kulob tara da ke da gurbi a cikin tawagarsu.
Sauran sun haɗa da Manchester City, da Chelsea, da Luton Town, da Wolves.
Lingard ya buga wa West Ham wasa a kakar 2020-21 a matsayin aro daga Man United.