Menu

Hare-haren 'yan bingida na neman durƙusar da yankin Gumau a Jihar Bauchi

54055644 Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro musamman a arewacin kasan

Mon, 21 Aug 2023 Source: BBC

Duk da cewa lamarin rashin tsaro ba baƙon abu ba ne a Najeriya, amma a yankin Gumau da ke Jihar Bauchi zai iya zama baƙo.

Mazauna garin Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a jihar ta Bauchi sun ce wani gungun ‘yan bindiga na kai hare-hare kan jama’ar wasu kauyuka tare da kashe su da kuma tafiya da dukiyoyinsu.

A bayan nan wasu rugage da wasu ƙauyukan Gumau ɗin sun fuskanci jerin hare-hare da suka yi sanadin mutuwar mazauna yankin.

Wani mutum da BBC ta tattauna da shi da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce " A sati biyu da suka gabata an zo garin Gumau an sace mutane har da wata yarinya mai ciki wata bakwai."

"An ɗauketa tare da maigidanta da kuma wani makwabcinsu, su uku aka tafi da su. Sai da suka biya kuɗin fansa sama da miliyan biyar sannan aka sake su," in ji mutumin.

Ya ce a ranar Juma'a sun shiga wani gari Mato mai nisan kilomita biyu zuwa uku daga Gumau, inda suka tarar da wani Alhaji suka karɓe kuɗaɗensa sannan suka kashe shi take.

"Bayan wannan a ranar Asabar sun sake shiga garin Gumau, suka ɗauki wani Alhaji wanda ya zuwa yanzu ba musan halin da yake ciki ba."

Yanzu dai rahotanni na cewa ana cikin yanayin tashin hankali a kauyen abin ya kai da wasu sun fara kwashe iyalansu suna barin Gumau.

Honorabil Jogo Isma'ila Haruna, shi ne ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, ya ce sama da kwana biyar sun samu labarin 'yan bindiga sun yi sansani a yankin su sama da 100, kuma ana tsammanin har da '' 'yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane" cikinsu.

Sun kai hari wani ƙauye da ake kira Ɓargar Fulani sun dauki "wani mutum sun kuma yanka wata mata har lahira sun kashe mutane da dama.

"Sun shiga garin Gumau sun ɗauki manyan mutane suna bin rugagen fulani suna kwashe shanun mutane da abinci, duk inda suka je sai sun kwashi abincin mutane sannan su ƙara gaba," in ji Ɗan Majalisar.

Ya ƙara da cewa manyan makamai suke amfani da su wajen kai hare-haren.

Ya ce sun firgita mutane da yawa ba sa iya kwana a gidajensu, duk sun bazama inda za su tsira da rayuwarsu.

Source: BBC