Kyeftin ɗin Liverpool, Jordan Henderson na duba yiwuwar komawa kungiyar da Steven Gerrard ke horasa wa wato Al-Ettifaq ta Saudiyya. Har yanzu dai ba su kai ga tuntubar ɗan wasan mai shekara 33, amma dai sun nuna sha'awarsa za su saye shi. (Telegraph, subscription needed)
Paris St-Germain za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta mallaki ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 29, duk da dai hankalinsa ya fi karkata ga Bayern Munich. (RMC Sport, in French)
Barcelona na son saye ɗan wasan tsakiya a Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 28, amma kuma suna son tuntubar ɗan wasan Tottenham da Argentina, Giovani lo Celso, mai shekara 27, koda za a samu matsala. (Mundo Deportivo, in Spanish)
Nottingham Forest na farautar ɗan wasan da suka jima suna zawarci wanda ke taka leda a PSV Eindhoven asalin Ivory Coast Ibrahim Sangare, mai shekara 25. (Athletic, subscription needed)
Liverpool a shirye take ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Chelsea da Ingila, Levi Colwill, mai shekara 20. (90min)
Manchester United da Newcastle United da Aston Villa na zawarcin ɗan wasan gaba a Atletico Madrid da Portugal, Joao Felix, mai shekara 23. (ABC, via Metro)
West Ham ta soma fusata kan cinikin ɗan wasanta na tsakiya Declan Rice, mai shekara 24, da take neman fan miliyan 105, sakamakon tsaikon da ake cin karo da shi daga ɓangaren lauyoyin Arsenal da ke shirya takardun kwantiragin. (Sky Sports)
Everton na son ɗan wasan Faransa Moussa Dembele, mai shekara 27, da kuma mai bugawa Leicester, Jamie Vardy, mai shekara 36. (FootballTransfers)
Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Leicester kan ɗan wasanta na gefe Harvey Barnes, mai shekara 25, kan fan miliyan £30. (Mail)
Ɗan wasan tsakiya a Nice da Wales Aaron Ramsey, mai shekara 32, ya samu tayi mai gwaɓi daga Saudiyya. (Sun)
Mai buga tsakiya a Tottenham da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 27, ya kasance matashin da Atletico Madrid ta jima tana zawarci. (Marca, in Spanish)
Chelsea a shirye take ta sayar da Trevoh Chalobah, mai shekara 24, a wannan kaka muddin ta samu tayi. (Evening Standard)
Manchester City ta yi watsi da tayin da aka gabatar mata na fan miliyan 30 kan ɗan wasanta da ke buga tsakiya James McAtee, mai shekara 20. (Sun)
Bristol City ta yi watsi da tayin fan miliyan 15 daga Bournemouth kan ɗan wasanta mai shekara 19, Alex Scott. (Bristol Live)
Mai tsaron baya a Manchester United Will Fish, ɗan shekara 20, ya amince ya sake komawa Hibernian zaman aro. (Manchester Evening News)
Wolves a shirye take ta karɓi tayi kan Jonny Castro Otto, mai shekara 29, yayinda take tattaunawa kan sake dawo da ɗan wasan Jamhuriyar Ireland, Matt Doherty, mai shekara 31. (Express & Star, subscription needed)
Ɗan wasan tsakiya a Chelsea da Amurka, Christian Pulisic, mai shekara 24, zai sanya riga mai lamba 11 idan ya koma AC Milan. (Goal)