Menu

Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta gayyaci Ganduje a kan 'bidiyon dala'

53095188 Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano

Fri, 7 Jul 2023 Source: BBC

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aika takardar gayyata tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a kan 'bidiyon dala'.

Wata sanarwa da hukumar ta PCACC ta fitar ta ce ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum da ake zargin cewa Ganduje ne lokacin da yake karɓar damin daloli yana zuba wa aljihu.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet ta fitar da bidiyon.

Sai dai Umar Abdullahi Ganduje ya sha musanta zargin, inda ya yi iƙirarin cewa abokan adawa ne suka shirya maƙarƙashiya da nufin hana masa damar shiga zaɓen 2019.

Lamarin dai ya janyo matuƙar ce-ce-ku-ce ba ma a Kano ba, har ma a Najeriya gaba ɗaya, abin da ya kai har majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin bincika gaskiyar lamarin.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen, Muhuyi Magaji Rimin Gado na cewa hukumar ta umarci tsohon gwamnan a kan ya bayyana gabanta cikin makon gobe.

Source: BBC