Menu

Hunter Biden na fuskantar tuhuma kan zargin kauce wa biyan haraji

Joe Biden Hunter Hunter Biden

Fri, 8 Dec 2023 Source: BBC

Masu shigar da ƙara na gwamnatin Amurka na tuhumar Hunter Biden kan zargin kauce wa biyan haraji, a karo na biyu da ake tuhumar ɗan shugaban ƙasar da aikata laifi.

Zarge-zarge tara ne ake tuhumarsa da su, da ke da alaƙa da kauce wa biyan haraji da ya kai dala miliyan 1.4 tsakanin 2016 zuwa 2019.

Manyan laifukan uku da ƙanana shida sun haɗar da gaza shigar da bayanai da biyan haraji, da yin ƙarya a bayanan haraji da kuma ƙoƙarin kauce wa biyan harajin baki ɗaya.

A watan Satumba ne aka tuhumi Mista Hunter Biden, mai shekara 53, kan zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba a Deleware.

A ranar Alhamis da daddare ne lauyansa ya ce sabbin tuhume-tuhumen da ake yi masa bi-ta-da- ƙullin siyasa ne kawai.

Ba a dai ambaci sunan mahaifinsa Shugaba Joe Biden a sabuwar tuhumar ba, kuma kawo yanzu fadar White House ba ta ce komai ba kan batun.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacoin da 'yan majalisar jam'iyyar Republican suka sanya batun kasuwancin Hunter a matsayin makamin da za su yi amfani da shi wajen buƙatar tsige shugaba Biden, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen shekara mai zuwa.

Idan kotu ta same shi da laifi kan batun, to zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 17 a gidan yari.

Lauyan ma'aikatar shari'ar ƙasar na musamman David Weiss na binciken Hunter - wanda ya yi karatun lauya a jami'ar Yale, sannan yake farfaɗowa daga jarabar shan koken tun 2019.

A cikin tuhumar mai hafi 56 da aka shigar a California, masu shigar da ƙara sun yi zargin cewa ya kashe kuɗaɗensa a kan ''ƙwaya, da mu'alama da mata masu zaman kansu da 'yan matansa, da manya-manyan hotel da gidajen haya da manyan motoci masu tsada, da tufafin alfarma da sauran abubuwan rayuwarsa, a taƙaice dai komai ciki har da haraji''.

Sun ce ɗan gidan shugaban ƙasar ''Ya karɓi fiye da dala miliyan bakwai na riba'' tsakanin 2016 zuwa 2020, amma ya gaza biyan harajin shekarar 2016 da 2017 da 2018 da kuma 2019 a kan lokaci, duk kuwa da cewa yana da kuɗin da zai iya biyan harajin''.

Lauyan Hunter Biden, Abbe Lowell, ya mayar da martani kan sabuwar tuhumar yana mai cewa "in da babu Biden a jikin sunan Hunter da ba za a yi masa tuhumar da aka yi masa a Delaware da kuma yanzu a Califonia ba.

Hunter Biden ya biya duka haraji da tarar da aka yi masa a shekara 2020, tare da taimakon lauyansa da ya ranta masa kuɗaɗe.

Bayanan da ke cikin tuhumar sun nuna abubuwan da Hunter ya kashe kuɗaɗensa a kansu.

tsakanin 2016 zuwa 2019, ya biya fiye da dala 188,000 kan ''nishaɗantar da matasa'', sannan fiye da dala 683,000 kan ''biyan mata masu yawa'', kamar yadda wani shafin tuhumar ya nuna.

Hunter Biden ''ya ci gaba da samun kuɗi masu yawa, sannan ya riƙa kashe su ta hanyar bushaha a 2018''. kamar yadda masu shigar da ƙarar suka yi zargi.

Tuhumar ta kuma ce Hunter ya samu ''gwaggwaɓar'' riba, musamman daga wani kamfani da ya kafa tare da wani ɗan kasuwar China, da wani kamfanin samar da wutar lantarki na Ukraine, Burisma da kuma wani ɗan kasuwar Romaniya da ba a ambaci sunansa ba.

Yayin da ribarsa ta ƙaru, sai ya ci gaba da kashe kuɗaɗen ta hanyar 'rayuwar almabazaranci'', in ji tuhumar.

A 2018, wanda ake zargin ya kashe fiye da dala miliyan 1.8, ciki har da dubban ɗaruruwan dalolin da ya fitar daga asusun banki, inda ya kashe kusan dala 383,000 wajen biyan mata, da dala 151,000 a kan tufafi.

Haka kuma a shekarar dai, Hunter Biden ya aike wa da tsohuwar matasarsa saƙon kar-ta-kwana cewa ba zai iya biyanta kuɗin ciyarwa ba ''saboda ba shi da isassun kuɗi''.

Ya kuma shafe lokuta yana zaune a manya-manyan hotel na alfarma, inda ya kashe dala 10,000 wajen biyan kuɗin rajista a wata ƙungiyar mazinata, sannan ya kashe dala 1,248 wajen sayen tikitin jirgi a faɗin ƙasar don halartar gidajen rawa, kamar yadda tuhumar ta yi iƙirari.

Masu shigar da ƙarar sun ce Hunter na da ''isassun kuɗaɗen da za su isa ya biya harajin da ke kansa da zarar lokacin biyan ya yi'', amma sai ya zaɓi ƙin biya.

An kuma zarge shi da gaza rubuta kuɗaɗen da ya kashe, kamar hayar wata mota ƙirar Lamborghini da ya yi amfani da ita a farkon lokacin da ya koma California a watan Afrilun 2018.

A wannan shekarar, masu kwarmata bayanai na hukumomin tattara haraji biyu suka tabbatar wa majalisar ƙasar cewa ya kamata a tuhumi Hunter da manyan laifukan kauce wa biyan haraji, amma daga baya suka yi zargin cewa an yi masa sassauci saboda shi ɗan shugaban ƙasa ne.

Haka kuma ya musanta aikata laifi a zargin mallakar bindiga da ake yi masa lokacin da yake ta'ammali da ƙwayoyi.

Kwamitin majalisar wakilan ƙasar da ke sanya idanu kan batun, na ci gaba da kiran tsige shugaba Biden, saboda zarginsa da hannu kan laifin ɗan nasa.

A yayin da 'yan majalisar jam'iyyar Repblican suka gabatar da takardun banki da suka ce suna tabbatar da cewa shugaba Biden ya yi ƙarya a lokacin da ya musanta amfana daga kasuwancin ɗan nasa, fadar White House ta ce gaba ɗaya zargin ba shi da tushe balle makama.

Source: BBC