Menu

IPOB: Kalaman Buhari kan masu tayar da hankali a yankin ƙabilar Igbo sun jawo zazzafar muhawara

 118774019 Buhari Governmentofnigeria Shugaba Muhammadu Buhari

Wed, 2 Jun 2021 Source: BBC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a kullum yana karɓar rahotannin hare-haren da ake kai wa cibiyoyin gwamnati yana mai cewa a bayyane yake cewa masu aikata hakan na son ganin gazawar gwamnatinsa ne.

Yayin da yake ganawa da jami'an hukumar zaɓe ta INEC a Abuja ranar Talata, Buhari ya ce matasan yanzu ba su san bala'in yaƙin basasa ba wanda aka yi a ƙasar daga shekarar 1967 zuwa 1970, har ma ya yi alƙawarin ɗaukar mummunan mataki a kan masu kai hare-haren.

A cewarsa: "Duk masu son lalata tsarin gwamnati za su sha mamaki kwanan nan. Mun ba su isasshen lokaci...Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa."

Sai dai waɗannan kalamai nasa ba su yi wa wasu daɗi ba, suna masu cewa a matsayinsa na shugaban ƙasa bai dace ya yi kalaman da suka yi kama da na tashin hankali ba.

A gefe guda kuma wasu na ganin wannan shi ne abin da ya dace tuntuni shugaban ya yi.

Abin da 'yan Najeriya ke cewa

Tun bayan yin kalaman nasa da misalin ƙarfe 5:30 na yamnmacin Talata a shafinsa na Twitter, sunan Buhari kawai ake gani a saman dandalin shafukan zumunta saboda yawan muhawara da maratni iri-iri da bayanan suka jawo.

An yi amfani da kalmar 'Buhari' sau fiye da 189,000 a Twitter ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Kazalika ana muhawarar ce da sauran kalmomi irinsu 'Boko Haram' da 'Genocide' wadda ke nufin kisan kiyashi, da 'civil war' wadda ke nufin yaƙin basasa, da 'Igbo' wato ƙabilar Ibo mazauna kudu maso gabashin Najeriya.

"Yaƙin basasar da ya kashe mutum kusan miliyan uku shekara 50 da suka wuce, da shi Buhari ke yi wa 'yan kudu maso gabas barazana a 2021 yayin da ake gyara halin 'yan Boko Haram kuma 'yan fashin daji ke kashe mutane. Abin mamaki," kamar yadda wani mai suna Uncle Ajala (@UNCLE_AJALA) ya wallafa a Twitter.



Shi kuma Adamu Hayatu (@AHayatu) cewa ya yi: "Suna ta basarwa da ɓoye al'amura shi kuma Buhari ya warware komai. Ku zubar da takardun karatunku ku zama dakarun Nnamdi Kanu shashashai."
Source: BBC