BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ina aka kwana kan ceto ƴanmatan Chibok bayan shekara tara?

Chibok Girls Har yanzu ba a gano ‘yan matan Chibok 96 ba bayan shekaru tara

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Shekara tara bayan sace ɗalibai mata kusan 300 daga makarantar sakandare ta Chibok, har yanzu babu labarin inda guda 96 suke.

A wata sanarwa da ƙungiyar Amnesty International ta fitar ranar Juma’a, a wani ɓangare na ranar tunawa da ranar da aka sace ɗaliban, ƙungiyar ta soki gwamnati bisa abin da ta kira ‘gaza kare su’.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekara ta 2014, lokacin da rikicin Boko Haram ya yi ƙamari a yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya, wasu mayaƙa suka kai farmaki a Makarantar Sakandare ta Chibok inda suka sace yara mata 276.

Daga baya sojoji sun samu nasarar ƙwato wasu daga cikin su, wasu kuma sun kuɓuta, yayin da ƙungiyar kuma ta sako wasu.

A sanarwar da ƙungiyar BBOG mai fafutikar ganin an ceto ɗaliban ta fitar domin tunawa da ranar, ta ce gazawar gwamnati wajen ceto yaran babban abin kunya ne.

Halin da ake ciki kan ceto ƴan matan Chibok

A cikin bayanin da ta fitar, ƙungiyar BBOG ta bayar da alƙaluma waɗanda ta ce su ne bayani na baya-bayan nan game da halin da yaran makarantar ta Chibok suke ciki tun bayan sace su a 2014.

-Yawan ɗaliban da aka sace: 276

-Yawan ɗaliban da suka tsere daga hannun mayaƙa: 57

-Yawan ɗaliban da mayaƙan suka saki: 107

-Yawan ɗaliban da sojoji suka ceto: 16

-Yawan ɗaliban da har yanzu ba a san inda suke ba: 96

Ci gaba da garkuwa da mutane

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar rikice-rikice na masu riƙe da makamai da kuma masu iƙirarin jihadi.

A tsakanin 2020 zuwa 2021 an samu rahotannin jerin munanan garkuwa da mutane a ƙasar, ciki har da waɗanda aka yi a makarantu.

Kamar na makarantar sakandaren Ƙanƙara da ke jihar Katsina, da na Kagara a jihar Neja, da Jangebe a jihar Zamfara, da Tegina a jihar Neja da kuma Yawuri a jihar Kebbi.

Irin waɗannan hare-hare sun tursasa rufe makarantu a jihohi da dama, musamman a arewacin ƙasar.

Amnesty International ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɗauki ƙwararan matakai wajen ganin ta kawar da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga irin su Boko Haram da ƴan fashin daji daga ƙasar.

Source: BBC