BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ina makomar David de Gea a Manchester United?

David de Gea

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Yayin da kwantragin mai tsaron ragar Manchester United David de Gea ta are a ranar Juma'a babu wanda zai iya hasashen makomarsa a Old Trafford.

An fahimci an samu sauyi kan yarjejeniyar da aka ƙulla tun da fari ta yiwuwar ƙara tsawaita kwantaraginsa da ƙungiyar idan wadda ake kai ta ƙare.

Wannan ya janyo daga dan wasan har ƙungiyar ko wa ya ƙi bayyana halin da ake ciki da inda aka nufa.

De Gea zai yi aure a ƙarshe makon nan abinda ya sa a samu jinkiri wajen tattaunawa tsakaninsa da ƙungiyar kenan har sai an kammala komai.

Dan wasan Sifaniyan mai shekara 32 ya kwashe shekara 12 a ƙungiyar Manchester inda ya buga wasa 545.

Rahotanni na cewa ɗan wasan zai iya sake haɗuwa da Cristiano Ronaldo a Saudiyya inda yake taka leda a yanzu.

Ƙungiyar Al-Nassr na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Sifaniya, bayan jin cewa kwantaraginsa ya ƙare a United.

Yayin da ake waɗannan jita-jita game da makomar ɗan wasan, de Gea ya sanya fuskar hamma a shafinsa na Twitter alamar gajiyawa kenan a farkon makon nan.

A ƙarshen kakar da aka kammala, ɗan wasan da ya taɓa zama wanda ya fi kowa ƙoƙari a United na shekara sau huɗu, ya lashe kyautar goaln da ya fi buga wasa ba a zura masa kwallo da yawa ba karo na biyu a jere, a wasa 17 kenan.

De Gea da kocin ƙungiyar Erik ten Hag sun tattauna a ƙarshen kakar nan, game da makomar golan a Manchester.

United na sanya ran ɗan wasan ya rage yawan ƙudin da ake biyan shi a mako na fan 375,000 kan yarjejeniyarsu ta 2019.

Source: BBC