BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ina matsayin ibadar mai azumin da ba ya sallah?

Addinin Musulunci ya wajabta sallah kan duk Musulmi

Wed, 29 Mar 2023 Source: BBC

Addinin Musulunci ya wajabta sallah kan duk Musulmi baligi kuma mai hankali a halin zaman gida ko na tafiya da yaƙi a kan namiji da mace - sai dai akwai uzuri a kan mace mai jinin al'ada da na biƙi.

Sallah ibada ce mai girma wadda ta kasance rukuni na biyu cikin rukunan Musulunci.

Ita ce ta raba tsakanin mutum da shirka da kafirci, kuma ginshiƙi ce ta rayuwar ibadar Musulmi.

Yayin da aka shiga azumin watan Ramadan mai alfarma, Musulmai kan ninka ko su ƙara riƙo da ibadunsu na farilla kamar sallah da sauran ayyukansu na alheri.

Amma akan samu wasu Musulman waɗanda ba sa tsayar da sallah yadda ya kamata, kuma irin wannan ɗabi'a takan ci gaba har cikin wata mai tsarki na azumi, duk da yake kuma suna azumin.

To ko mene ne matsayin mai azumin da ba ya sallah?

BBC ta tuntuɓi Dr Zahra'u Muhammad Umar, wata malamar addinin Musulunci a Kano, wadda ta bayyana muhimmancin tsayar da sallah.

"Idan kuna azumi, ba kwa sallah, kun rusa addininku ne baki ɗaya." in ji Dr Zahra'u.

A cewarta, "ba za a ce ladan azumi kwata-kwata babu shi ba, tun da kowanne sha'anin addini, harkarsa daban.

Amma idan aka duba sigar sallah ɗin yadda ta zo, ita ce ginshiƙin addini, to ya za a yi, a yi azumi ba a sallah, har kuma a yi tunanin azumi yana nan daidai?

"Abin da dai ake so, Aljannar Allah ake so, so ake a tafi wurin Allah da kyakkyawan sakamako, toh wanda yake ginshiƙi ba ka yi shi ba, kana azumi ba ka yin ginshiƙin da zai tabbatar da kai Musulmi ne, kada ka ɗauka azuminka na da wata fa'ida - ba shi da fa'ida." in ji ta.

Ta kuma ce sai idan mutum yana sallah ne zai sa ran azuminsa zai karɓu a wajen Allah.

Shi ma, Mallam Yusuf Usman Kofa, Babban Limamin Masallacin Ansar a Kano, ya ce babu amfani mutum ya yi azumi, ba ya sallah saboda ba zai amfane shi ba.

"An gina addinin Musulunci ne a kan muhimman ginshiƙai guda biyar - Kalmar Shahada da Sallah da Zakkah da Azumi da Hajji." in ji Malamin.

Ya ce duk Musulmin da ya tsayar da sallah, to kuwa ya tsayar da addini ne.

"Idan sallah ta cika, to komai zai zo da sauƙi, idan aka samu matsala a sallah, to babu yadda za a yi, a tsallake."

A cewarsa, babu yadda za a yi mutum ya samu tsira da yin azumi kawai babu sallah.

Amma azumi a wani lokacin akan yi afuwa a rama ko a ciyar, amma ita sallah babu wani hali da ake ɗauke wa mutum ita.

Ko da yanayin rashin lafiya ne an ce sai mutum ya yi ta ko da a zuciyarsa ne saboda girman matsayinta da ƙimarta," in ji malamin

Yaya ladan azumin wanda ba ya sallah?

Dr Zahra'u ta ce zai yi wuya kai tsaye a ce azumin wanda ba ya sallah bai karɓu ba saboda "Ba kai ne Mahalicci ba, mutum ba shi da izinin yanke wannan hukunci."

"Zai iya yiwuwa mutum ya yi azumi daidai, kuma sallolin da bai yi ba, ya zo ya tuba ga Allah, kuma ya rama su, azuminsa na nan daram, harkarsa kuma ta dawo daidai".

Malamar ta ƙara bayyana irin girman laifin da ke tattare da rashin yin sallah musamman ga wanda ke azumi.

Ta ce makomar mai irin wannan halayya tana wajen Ubangiji.

A cewar Mallam Yusuf Usman Kofa, duk wanda ba ya sallah, azuminsa ba zai zama karɓaɓɓe ba saboda "Ma'aiki SAW cewa ya yi, wanda bai bar faɗin ƙarya ba, ko aiki da ƙarya ba, Allah ba Shi da buƙatar aikinsa na daina ci da daina sha da ya yi da sunan azumi,"

Ya ƙara da cewa azumi ba zai yi tasiri ga wanda ba ya sallah ba.

Matsayin mai wasa da sallah a lokacin azumi

Malama Zahra'u ta kuma taɓo Musulman da ke jinkirin yin sallah - wato yin sallah ba a kan lokaci ba inda ta bayar da misali da ma'aikata da kuma mata da suke duƙufa wajen aikin ofis ko kuma hidimar girki don buɗa baki.

Ta ce: "Mai wasa da sallah zai shiga cikin garari, zai shiga cikin azabar Allah."

A cewarta, rashin tsari ne ke janyo irin wannan sakacin saboda muddin mutum ya tsara yadda ayyukansa za su gudana kuma ya nemi taimakon Allah, harkokinsa za su tafi daidai, ba tare da ya tauye muhimman ibadun da suka rataya a wuyansa ba.

"In dai kana da tsari, ba yadda za a yi ka kauce wa yin sallah a kan lokaci" in ji Dr Zahra'u.

Shi kuwa, Mallam Yusuf Usman Kofa cewa ya yi, yin hakan hatsari ne na gaske saboda a cikin Suratul Maaun, Allah SWA ya ce "Azaba ta tabbata ga masu sallah, waɗanne? sai ya ce "waɗanda a cikin sallarsu suke sakaci da ita, sakaci ta ɓangaren idan lokacinta ya yi, ba sa yi, ko suna fifita wani abu a kanta."

Ya bayar da misali da Umar Bn Khattab wanda ya umarci gwamnoninsa su fifita sallah saboda ita ce lamarinsu na sauke haƙƙi a wajena shi ne lura da sallah ta al'umma.

Ya ce "wulaƙanta sallah da ƙin yinta a kan lokaci abu ne na laifi mai girma, babu uziri mutum ya bari lokacin sallah ya fita - a cikin malamai akwai waɗanda suka ce ba a buƙatar ka rama, zunubin mutum sai ya je wajen Allah,"

"Saboda duk maganganu ko hadisai da suka zo a kan ramuwar sallah, ga wanda ya manta ne, ba ga wanda yana sane lokaci ya wuce ba, shi wannan ba a buƙatar ya rama, sai an haɗu a gaban Allah." kamar yadda Malamin ya bayyana.

Source: BBC