BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Inter ta kai daf da karshe duk da tashi 3-3 da Benfica a Champions

Lautaro Martinez

Thu, 20 Apr 2023 Source: BBC

Inter Milan ta kai karawar daf da karshe a Champions League, duk da ta tashi 3-3 a wasa na biyu zagayen quarter finals ranar Laraba.

Inter wadda ta ci 2-0 a Portugal a wasan farko ranar Talata 11 ga watan Afirilu ta kai zagayen gaba da cin kwallo 5-3 gida da waje kenan.

A karawar da suka yi a Italiya ranar Laraba, Inter ce ta fara cin kwallo minti 14 da take leda ta hannun Nicolo Barella, yayin da Benfica ta farke tun kan hutu ta hannun Fredrik Aursnes.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Inter ta kara biyu ta hannun Lautaro Martinez da kuma Joaquin Correa

Kungiyar Portugal ta kara sa kaimi, inda ta zare ta biyu saura minti hudu a tashi daga wasan ta hannun Antonio Silva, sannan Petar Musa ya farke na uku daf da za a tashi.

Akwai karin bayanai....

Source: BBC