Inter Milan ta lashe kofin Serie A na 2020/2021 a karon farko tun bayan shekara 11, duk da saura wasa hurhudu a karkare kakar bana.
Hakan ya kawo karshen Juventus wadda ta yi kaka tara a jere tana lashe kofin gasar Italiya.
Inter Milan ta ci kofin ne, bayan da Atalanta wadda ake ganin tana cikin 'yan takara ta kasa cin Sassuola da suka tashi 1-1 ranar Lahadi.
Hakan ya sa Atalanta ta hada maki 69 a mataki na biyu iri daya da na Milan ta uku da tazarar maki 13 tsakaninsu da Inter.
Inter wadda ta doke Crotone da ci 2-0 ranar Asabar za ta iya bikin lashe Serie A na bana da ta yi a karon farko tun bayan 2009/10 karkashin Jose Mourinho.
Inter ita ce ta yi ta biyu a bara da Juventus ta lashe Serie A na tara a jere.
Wannan shi ne Serie A na hudu da Antonio Conte ya lashe, bayan cin uku a jere a Juventus a lokacin da ya horar da ita tsakanin 2011 zuwa 2014.
Haka kuma ya ja ragamar Chelsea ta dauki Premier League a kakar farko da ya karbi aiki a 2017.