BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Isra'ila-Gaza: Me ya sa wannan yaƙi ya zama daban da sauran

56871449 Hoton alama

Fri, 17 Nov 2023 Source: BBC

Da a ce wannan yaƙin na Gaza kamar duk sauran ne, zuwa yanzu mai yiwuwa da an samu tsagaita wuta.

Mutanen da suka rasu, da an binne su, kuma da Isra'ila ta fara gardama da Majalisar Ɗinkin Duniya a kan yawan sumuntin da za a kai Gaza don sake gina gidajen da aka ruguza.

Sai dai wannan yakin ba kamar wadancan ba ne, ba kawai saboda yawan kashe rayukan da ake yi ba, a farko na Hamas ranar 7 ga watan Oktoba, wanda akasari ya kare a kan fararen hulan Isra'ila.

Sai kuma abin da ya biyo baya na "babbar ramuwar gayya" kamar yadda Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana, wadda ta kashe akasari fararen hula Falasdinawa.

Wannan yaki yana da bambanci da sauran saboda ya zo ne sa'ar da batutuwan da suka raba kan kasashen Gabas ta Tsakiya, suka kara zurfi.

Ga tsawon akalla shekara ashirin, mafi tsananin rarrabuwar kan da ta kai ga karyewar shimfidar tsarin yankin, ya kasance tsakanin abokai da kawayen Iran da kuma abokai da kawayen Amurka.

Gamayyar abokan kawancen Iran da a mafi yawan lokuta ake kira "tungar bijirarru", ta kunshi Hezbollah a Lebanon da gwamnatin Assad a Siriya da mayaka 'yan tawayen Houthi na Yemen da hade-haden sojojin haya na Iraqi da Iran ta bai wa makamai sannan ta horas da su.

'Yan Iran suna kuma goyon bayan Hamas da kungiyar Islamic Jihad na Gaza.

Iran na kuma kara kusantar Rasha da China.

Ta kuma zama wani ginshiki a kokarin yakin da Rasha take yi a Ukraine. China na sayen man fetur din Iran mai tarin yawa.

Dadewar da yakin Gaza zai yi, da kuma karin kashe-kashen Isra'ila kan Falasdinawa fararen hula da ruguza dubun dubatar gidaje, irin girman hatsari da wannan rikici yake da shi, na shigar wasu wakilai daga wadannan bangarori guda biyu.

Al'amura a kan iyaka tsakanin Isra'ila da Lebanon na kara zafi, sannu a hankali amma ba kakkautawa. Daga Isra'ila har Hezbollah babu mai son shiga wani sabon cikakken yaki. Sai dai yayin da suke kara kintsawa juna babban naushi, hatsarin ta'azzara yakin babu kakkautawa zai dada girmama.

Mayakan Houthi a Yemen suna harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa Isra'ila. Duka dakarun tsaron saman Isra'ila da jiragen ruwan yakin sojojin Amurka sun kakkabo su kasa zuwa yanzu a Tekun Maliya.

A Iraƙi, sojojin hayan da Iran ke tallafawa sun kai hari kan sansanonin Amurka. Amurka ta mai da martani kan wasu cibiyoyinsu a Siriya. Haka kuma, duk ɓangarorin na ƙoƙarin taƙaita haɓakar yaƙi, amma iyakance ruruwar matakin soja a ko da yaushe abu ne mai wahala.

A ɓangaren Amurka, akwai Isra'ila da ƙasashen Gulf masu arziƙin man fetur, sai Jordan da kuma Masar. Amurka na ci gaba da nuna gagarumin goyon baya ga Isra'ila, ko da yake a bayyane take ƙarara cewa Shugaba Joe Biden ba ya jin daɗin yadda Isra'ila take kashe Falasɗinawa fararen hula da yawa. Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya faɗa a bainar jama'a cewa ana kashe Falasɗinawa fararen hula masu yawa.

Larabawa abokan ƙawancen Amurka duk sun yi tofin Allah tsine kan abin da Isra'ila take yi kuma sun yi kiran a tsagaita wuta. Ganin dubun dubatar Falasɗinawa suna gujewa gidajensu a arewacin Gaza inda suke niƙar gari a ƙafa kan manyan tituna zuwa kudu, ya taso da fatalwar nasarar Isra'ila a kan Larabawa a yaƙinta na samun 'yancin kai cikin 1948.

Falasɗinawa fiye da 700,000 ne suka tsere ko kuma 'yan Isra'ila suka tilasta barin gidajensu da tsinin bindiga, a lamarin da Falasɗinawa suke kira da Nakba - bala'i. 'Ya'yan 'yan gudun hijirar 1948 sun haɗar da jama'a mai yawa na Zirin Gaza.

Maganganu masu hatsari daga wasu Yahudawa masu tsananin kishin ƙasa da tsattsauran ra'ayi da ke goyon bayan gwamnatin Benjamin Netanyahu ta saukar da wani bala'in ko Nakba a kan Falasɗinawa, yana tayar da hankalin ƙasashen Larabawan da ke ɓangaren Amurka, musamman Jordan da ƙasar Masar. Wani minista a gwamnatin Netanyahu har ya fara batun a jefa wa Gaza bam ɗin nukiliya don a yi maganin Hamas. An tsawatar masa a kan wannan kalami amma ba a kore shi daga muƙaminsa ba.

Duk wannan ana iya yin watsi da su a matsayin maganganun shiririta na wasu sakarkaru kawai, amma ana ɗaukansu da gaske a Jordan da kuma Masar. Ba wai maganar makaman nukiliya ba, waɗanda Isra'ila ke da su masu yawan da ba ta taɓa bayyana adadin da ta tara ba, amma yiwuwar a tilasta wa Falasɗinawa tserewa daga yankunansu zuwa kan iyakoki.

Dangane da shi kansa yaƙin na Gaza, manyan jami'an diflomasiyyar Ƙasashen Yamma kama daga manyan abokan ƙawancen Isra'ila, sun faɗa wa BBC cewa kawo ƙarshen yaƙin da kuma tunkarar bayansa zai kasance abu mai "wahala da damalmalewa".

Wani ya ce "hanyar da kawai za ta ɓulle ita ce a sake gina wani ginshiƙin siyasa ga Falasɗinawa". Hakan na nufin kafa wata ƙasar Falasɗinu mai 'yancin cin gashin kanta a gefe guda da Isra'ila, masalahar da ake cewa kafa ƙasa biyu, wani kasasshen tunani da ake jin amonsa a wani take.

Bitar shi, mai yiwuwa a yanayi na haƙura da ɗumbin abubuwa tsakanin Isra'ila da Larabawa, wani shiri ne na ci-da-zuci, ko da yake mai yiwuwa shi ne tunani mafi dacewa da ake da shi. Sai dai a halin da ake ciki na zafin ciwo da tashin hankali da kuma ƙiyayya, zai yi wuya a iya aiwatarwa.

Hakan dai ba zai faru ba a ƙarƙashin shugabancin yanzu na Isra'ila da na Falasɗinawa.

Firaminista Netanyahu dai bai bayyana shirinsa ko da na kwana guda bayan kawo ƙarshen yaƙi a Gaza ba, sai dai ya yi watsi da tunanin Amurka na kafa wata gwamnati ƙarƙashin Hukumar Falasɗinawa, da Shugaba Mahmoud Abbas ke jagoranta, wadda Hamas ta fatattaka daga Gaza a 2007.

Ɓangare na biyu na shirin Amurka shi ne hawa teburin tattaunawa don cimma masalahar kafa ƙasa biyu, wani abu da Benjamin Netanyahu ke adawa da shi a tsawon tarihin siyasarsa.

Ba kawai Mista Netanyahu adawa yake da kafa 'yantacciyar ƙasar Falasɗinawa ba ne.

Tsiransa a matsayin firaminista, ya dogara ne a kan goyon bayan da yake samu daga Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi waɗanda suka yi imani cewa ɗaukacin yankin tun daga kogin Jordan har zuwa Bahar Rum, Allah ne ya fawwala wa al'ummar Yahudawa, kuma duka kamata ya yi a ce suna cikin iyakokin Isra'ila.

Da yawan 'yan Isra'ila na son ganin bayansa, inda suke zarginsa da gazawar tsaro da ta tattara bayanan sirrin da suka ba da damar kai hare-haren 7 ga watan Oktoba.

Shugaban Falasɗinawa Abbas yana cikin shekarunsa na 80 kuma ba shi da ƙima a idanuwan masu niyyar yin zaɓe, ko da yake bai iya gabatar da kansa ga masu zaɓe ba tun shekara ta 2005. Hukumar Falasɗinawa tana aiki tare da Isra'ila kan sha'anin tsaro a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan amma ba ta iya kare jama'arta daga Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna masu ɗauke da makamai.

Da canjin shugabanci daga bisani. Idan wannan ƙazamin yaƙin na Gaza bai tilasta wa 'yan Isra'ila da Falasɗinawa da kuma abokan ƙawancensu masu ƙarfi wajen sake cimma zaman lafiya ba, to abin da kawai zai faru a nan gaba shi ne wasu yaƙe-yaƙe.

Source: BBC