Menu

Jadawalin wasannin cike gurbi na Euro 2024

45013685 Yan wasan Ingila

Thu, 23 Nov 2023 Source: BBC

Wales za ta karɓi baƙuncin Filland a wasan cike gurbi na gasar Euro 2023 da Jamus za ta karɓi baƙunci.

Wanda ya yi nasara cikinsu zai buga wasan gaba da Poland ko Estonia a gida domin samun gurbi a gasar da za a fara a ranar 14 ga watan Yuni a ƙare a ranar 14 ga watan Yuli 2024.

A rukuni na biyu akwai wasa tsakanin Isra'ila da Iceland, yayin da Bosnia Herzogovina za ta karbi baƙuncin Ukraine.

A rukuni na uku Georgia da Luxembourg ne za su fatata wadda ta yi nasara kuma za ta barje gumi da Kazakhstan ko kuma Greece.

Tawaga 20 ta samu gurbin shiga gasar Euro 2024 kai tsaye, inda Jamus za ta karbi bakuncin wasannin a 2024.

Dukkan wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni, sune suka samu tikiti kai tsaye a wasannin da za a fara daga Yuni zuwa Yulin 2024.

Yanzu kenan saura gurbi uku ya rage, inda tawaga 12 za ta buga wasannin cike gurbin shiga Euro 2024.

Cikakken jadawalin wasannin cike gurbin

Rukunin A

Poland vs Estonia

Wales vs Finland

Rukunin B

Israel vs Iceland

Bosnia-Herzegovina vs Ukraine

Rukunin C

Georgia vs Luxembourg

Greece vs Kazakhstan

Tawaga nawa ce za ta buga Euro 2024?

Kasa 12 ce za ta barje gurbi a Euro 2024, inda Jamus da za ta karbi bakuncin wasannin ce kadai da ta samu takiti kai tsaye.

Ranar Talata aka kammala karawar cikin rukuni ta yadda aka samu 20 da suka kai Euro 2024 kai tsaye

Kawo yanzu su waye suka samu gurbin Euro 2024?

Spain

Scotland

France

Netherlands

England

Italy

Turkey

Croatia

Albania

Jamhuriyar Czech

Belgium

Austria

Hungary

Serbia

Denmark

Slovenia

Romania

Switzerland

Portugal

Slovakia

Source: BBC