Jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko, wanda aka kama a ranar Juma'a, ya sanar da fara yajin cin abinci.
Ya yi kira ga duk wadanda ake tsare da su a gidajen yari saboda siyasa su mara masa baya.
A wani sako da aka wallafa a shafukansa na sada zumunta, Mista Sonko ya ce a yayin da ƴan kasar ke fuskantar danniya da tsangwama, ya yanke shawarar bijirewa.
Yana dai fuskantar tarin sabbin tuhume-tuhume, ciki har da kokarin haifar da tashin tashina, da hurewa matasa kunne, da kuma kwace.
A wani taron manema labarai a Dakar babban birnin kasar, daya daga cikin lauyoyinsa Koureychi Bâ, ya ce Mista Sonko ya samu goyon bayan wasu fursunoni don fara yajin cin abincin tare da su.
A cewarsa "Tun bayan yanke hukuncin da Mista Sonko ya yi na fara yajin cin abinci, mun samu labarin cewa a wasu gidajen yari da ke Senegal, daurarru sun kuduri aniyar mara masa baya, don fara wannan yajin cin abinci’’.
Kama Mista Sonko, da kuma shari’arsa kan wasu zarge-zarge a baya bayan nan dai, sun haifar da tashe-tashen hankula, har ta kai ga janyo mutuwar mutane 16 a cewar alkaluman gwamnati, 24 a cewar Amnesty International, 30 a cewar bangaren jagoran ‘yan adawar.
A wani mataki na kan da garkin abun da ka iya faruwa a wannan karon, ofishin jakadancin Amurka da ke Senegal ɗin, ya bukaci ƴan Amurka su kasance cikin shirin ko ta kwana.