Menu

Jihar Katsina: An dakatar da hakimi saboda zargin alaƙa da 'yan fashin daji

 118287469 617e6476 Ac8b 485b 8d04 0f0eb9b017e2 Mai Martaba, Sarki Abdulmumini Kabir Usman, Mai Masarautar Katsina

Sun, 2 May 2021 Source: BBC

Masarautar Katsina ta dakatar da Sarkin Fawwa, kuma hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, dangane da wasu korafe-korafe da suka fito daga al'ummar yankin Kankara da kuma jami'an tsaro, bisa zargin da ake yi masa na alaka da 'yan fashin daji da suka addabi jihar.

Masarautar Katsina ta ce ta dauki wannan mataki ne domin jaddada wa gwamnati da al'umma cewa tana goyon bayan yaki da ta'addanci da mahukunta ke yi a dai dai wannan lokaci.

Tuni masarautar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa hakimin na Fawwa Alhaji Abubakar Yusuf.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun hadar da hada baki da yan sa kai wajen aikata wasu abubuwa da ba a fito fili an bayyana ba.

Alhaji Mamman Iso, Sarkin Yakin Katsina, kuma sakataren masarautar Katsina, ya shaida wa BBC cewa babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi na cewa ana yi wa hakimin bi ta da kulli ne.

Ya ce idan kwamitin da aka kafa ya kammala bincike zai gabatar da rahotonsa wanda za a aika wa gwamnati, sannan idan har an gano cewa bai aikata laifin komai ba za a bayar da umarnin mayar da shi kan kujerarsa nan take.

Jihar Katsina da Zamfara mai makwabtaka da ita dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalolin tsaro da ake alakantawa da yan fashin daji a wannan lokaci.

Ko da a baya mahukunta a wadannan jihohi biyu sun sha daukar matakin korar masu rike da sarautun gargajiya da ake zargin suna hada baki da maharan da suka addabi jama'a ta hanyar kai hare hare garururwa da kuma satar mutane.

Duk da cewa mahukunta kan ce suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki, bayanai na nuna yadda ake samun karuwar hare-hare da satar mutane, abin da ke nuni da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

Source: BBC