Menu

Jirgin Belarus: Me ake nufi da ƙwace jirgin fasinja a sararin samaniya?

 118655628 Mediaitem118655627 Belarus ta aika jirgin soja don ya sauya wa wani jirgin fasinja hanya domin kama wani dan jarida

Wed, 26 May 2021 Source: BBC

"Idan jirgin soja ya ƙwace ka kuma ya ba ka umarni, biyayya za ka yi". Wannan ne ra'ayin wani matuƙin jirgin sama wanda ya yi magana da BBC, wanda ya ce matakin Belarus na tursasa wa wani jirgin dakon mutane "haɗari ne".

Belarus ta aike wani jirgin yaƙi don ya sauya wa wani jirgin Ryanair hanya - wanda ya taso daga Girka zai je Lithuania - ya sauka a Minsk ranar Lahadi, inda ta ce ai akwai wani abun fashewa a cikin jirgin. Sai dai ba a gano shi ba.

Ƴan sanda sun yi awon gaba ɗan jarida mai goyon bayan ɓangaren adawa Roman Protasevich lokacin da jirgin ya sauka a babban birnin Belarus. Filin jirgin ba ya cikin jadawalin masu tuƙa jirgin.

Masana a harkar jiragen sama sun ce wannan wani "babban al'amari ne a diflomasiyya" wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.

Idan jirgin sama ya keta hazon ƙasashen duniya, jirgin yana da shaidar zama ɗan kasar da aka yi masa rajista.

A wannan karon, jirgin na Ryanair na da rajistar ƙasar Poland ko kamfanin "Ryanair Sun", wani ɓangare na kamfanin jirgin sama na kasar Ireland. Idan jirgin na tafiya a sama, ba tare da dogaro da a dai-dai ina ya ke ba, asalinsa Poland ne.

"Ƙwace jirgi a lokacin da yake sama lamari ne na diflomasiyya da ya ƙunshi ƙasar da aka yi masa rajista, a cewar wani babban masanin harkokin jiragen sama.

Wani matuƙin jirgi ya ƙara da cewa "wannan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da yawa".

Dokar da ke bai wa jirage damar wucewa ta saman ƙasashe ba tare da sun sauka ba ita ce "Dokar Farko ta Ƴancin Sararin Samaniya" kuma wannan ƴancin na da muhimmanci wajen bai wa fasinjoji da sauran jirage zuwa daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar a faɗin duniya.

Matakin Belarus na ƙwace jirgin fasinjoji a sararin samaniya da tursasa masa sauka a wata ƙasa ya karya doka. Bisa wannan dalilin ne shigaban Ryanair, Michael O'Leary ya bayyana lamarin a matsayin "fashin da wata ƙasa ta dauki nauyinsa".

Amma Belarus ba ta sa hannu kan yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta hulɗar jirgin sama ba.

Yaushe ne sojoji ke iya ƙwace jirgi?

Ƙwace jirgi na faruwa ne musamman saboda dalilai na tsaro a cewar masana. Idan fasinjojin da ke cikin jirgin da waɗanda ke garuruwan da ke ƙasa na cikin haɗari, sai ƙasar ta ɗauki matakin da ya kamata.

Idan cibiyar da ke kula da kai-komon jirage ta rasa hanyoyin sadarwa da ko wane jirgi, ma'aikatan cibiyar za su yi ƙoƙarin lalubo jirgin sun yi magana da matuƙinsa. Amma idan suka gaza ganowa bayan gawadawa sau biyu, ana iya aika jirgin soji.

"Jirgin yaƙin zai zo ya jawo hankalin jirgin fasinjoji kuma ya samu damar isar da saƙon cewa ya kira cibiyar sannan ya tabbatar da cewa ba ƙwace ragamar jirgin aka yi ba ko kuma jirgin na daf da faɗuwa a wani babban birnin ne.

"Cibiyar na shiga fargaba idan ta daina jin ɗuriyar jirgi tun bayan hare-haren 9/11", a cewar wani matuƙin jirgin.

Ko kuma idan matuƙin jirgin ya isar da saƙo ta wayar sadarwar da ke cikin jirgin don sanar da cewa jirgin na cikin matsala, ana iya aika jirgin yaki.

Me ke faruwa a lokacin da jirgin soji ya ƙwace jirgi?

Idan aka tura jiragen sojoji su ƙwato jirgin fasinjoji a sama, na sojojin na shiga gaba a jere sai na fasinjojin ya biyo su.

Kuma a wannan lokacin jiragen sojin za su riƙa ƙoƙarin gano jirgin fasinjojin ta hanyoyin sadarwa ta musamman.

Idan suka gaza samo jirgin, akwai wasu hanyoyin da ake bi.

"Suna haska fitilinsu da dare. Da rana kuma suna motsi da fika-fikansu kuma haka na nufin jirgin fasinjojin ya bi su a baya, kuma dole ya bi," a cewar matukin jirgin.

Jirgi ya shiga matsala tare da fasinjoji

Ko wane jirgi yana da shirinsa da ya ke shigarwa Eurocontrol. Wannan ya ƙunshi komai, kama daga tashi daga titin jirgin zuwa sauran abubuwan da ke gudana a lokacin da ya ke sama da saukarsa. Amma ƙwace jirgin na nufin an rusa duka wannan shirin.

"Matuƙin jirgin zai shiga tsananin damuwa don bai san abin da ke faruwa ba. Bai kuma san inda za a je ba," a cewar wani matuƙin jirgi na wani babban kamfanin jirgin sama a Najeriya.

Matsalar ita ce a ƙwace jirgi irin wannan, matuƙin jirgin bai shirya wa hanyar da za a sa shi ya bi ba, don haka an shiga haɗari gaba ɗaya.

A yanzu an hana jiragen Burtaniya bin hanyoyin sama na Belarus.

Akwai sauran bayanai da ba a sani ba dangane da ƙwace jirgin a Belarus, ciki har da cikakkun bayanai na lokaci da yadda abin ya faru da safiyar Lahadi.

Amma ga kamfanin jirgin da fasinjoji biyu da gaba ɗaya nahiyar, wani babban al'amarin diflomasiyya na gudana.

Saboda tsaro da harkokin diflomasiyya dangane da wannan lamari, masana a harkokin jiragen sama ba sa so a bayyana sunayensu a wannan maƙalar.

Bayanai dangane da Belarus

Ina ne Belarus?

Ƙawarta Rasha na gabashinta kuma Ukraine na kudanci. A arewacinta da yammacinta kuma Tarayyar Turai da ƙasashe mambobin Nato Latvia da Lithuania da Poland.

Me ya sa ya ke da muhimmanci?

Kamar Ukraine, wannan ƙasar mai mutum miliyan 9.5 na tsakiyar hamayyar da ke tsakanin ƙasashen Yamma da Rasha.

An yi wa Shugaba Lukashenko laƙabi da "Mai Mulkin Kama Karya na Tura mafi shahara" - shekararsa 27 a mulki.

Me ke faruwa a can?

Akwai wani gangami na hamayya mai girma da ke buƙatar sabon shugabanci na dimokuraɗiyya da sabbin manufofi na tattalin arziƙi.

Ɓangaren adawa da gwamnatocin Yamma sun ce Mista Likashenko ya yi maguɗi a zaɓen 9 ga Agusta. A hukumance ya lashe zaɓen da gagarumar nasara.

Source: BBC