Menu

Jordi Alba ya koma Inter Miami daga Barcelona

Jordi Alba

Wed, 19 Jul 2023 Source: BBC

Mai tsaron bayan tawagar Sifaniya Jordi Alba ya koma Inter Miami da taka leda, in ji shugaban ƙungiyar Jorge Mas.

Mas ya ce tuni tsohon dan wasan Barcelona mai shekara 34 ya saka hannu kan kunshin yarjejeniya zai kuma buga karawar da kungiyar za ta yi da Atlanta.

Alba zai taka leda tare da tsoffin 'yan wasan Barcelona da suka koma Inter Miami da suka hada da Lionel Messi da kuma Sergio Busquets.

Mai tsaron bayan ya bar Barcelona a karshen kakar da ta wuce bayan ya ci kwallo 27 a wasa 459 da ya yi cikin kaka 10 a kungiyar Camp Nou.

Alba ya bayar da gudunmuwar da Barcelona ta lashe La Liga shida da kuma daukar Champions League a 2015.

Messi kyaftin din Argentina da Busquets sun saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a 2025 a Inter Miami.

Ranar Lahadi Inter Miami ta gabatar da Messi da Busquets gaban magoya bayanta 20,000.

Messi mai rike da Ballon d'Or bakwai ,ya yi atisaye tare da 'yan wasan Inter Miami a karon farko ranar Talata - ana sa ran zai fara buga mata tamaula ranar Juma'a.

A Juma'ar ne Inter Miami za ta buga Leagues Cup, inda za ta fuskanci Cruz Azul ta birnin Mexico.

Source: BBC