Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi 'yan kasar. Wannan shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane da shirin manyan zaɓukan da ƙasar za ta gudanar daga watan Fabrairun 2023. Fannonin da za a yi duba a kai din su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci. Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu wallafa 25 ne kawai, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022. Matsalar tattalin arzikin da ƙasashen duniya ke ci gaba da fuskanta na ƙara ta'azzara a wasu ƙasashe kamar Najeriya, inda wasu bala'o'i ke ƙara zafafa lamarin. Ambaliyar ruwan da wasu jihohi ke fuskanta a daminar bana ta ƙara wa wasu al'ummomi tsadar rayuwa kasancewar ta katse hanyoyi mafiya sauƙi da mutanen ke bi don yin zirga-zirgar yau da kullum. Irin wannan lamari ne ya faru ga mutanen yankin Birnin Kudu na Jihar Jigawa a arewacin Najeriya, inda gadar da ke sada su da Jihar Kano ta karye. Sai dai mazauna yankin sun shafe fiye da shekara ɗaya a cikin matsalar, inda ta tilasta wa 'yan kasuwa da ke saye da sayarwa a tsakanin jihohin yin zagaye. Wannan maƙala ta ƙunshi labaran ma'abota BBC Hausa uku, waɗanda suka bayyana mana yadda matsalar tattalin arziki ke shafar rayuwarsu a yankunansu. 'Kuɗin motar da muke kashewa ya ninka sau huɗu' Musa Garba ɗan kasuwa ne da ke zaune a Jihar Kano wanda kuma yake safarar kaya daga Kano zuwa Birnin Kudu na jihar ta Jigawa. Malam Musa da sauran matfiya kan bi ta gada mai lamba A237 wadda ke haɗe jihohin. Sai dai gadar ta karye tun a 2021, abin da ya sa matafiyan suka koma zagaye kuma kuɗin mota suka ninninka. "Wannan zagayen ne ke jawo kashe kuɗi, inda muke kashe N500 maimakon N150 da a da take biya mana buƙata," a cewarsa. Ya ƙara da cewa a da hanya ce ɗoɗar ake wucewa. "Da yake da ma idan mun zo a Kwanar-Huguma muke sauka sai mu hau ta Birnin Kudu, wanda bai wuce N150 ba, amma yanzu sai mun biya N500 zuwa N600, saboda zagayen da ake yi ta Kiyawa sannan a ɓullo Birnin Kudu." Musa ya ce wannan matsala ta sa ya dakatar da kasuwancin nasa da kuma wasu 'yan kasuwar ma da yawa. "Wannan dalilin ya sa muka dakatar da kasuwancin ma, duk da cewa akwai wasu hanyoyin da ake bi amma daji ne, mutane na tsoron bin su saboda matsalar tsaro." 'Na jingine ginin gida da aure saboda tsadar rayuwa' Cikin sanyin murya da fawwala wa Allah lmauransa, matashi Musa Saleh ya faa wa BBC Hausa cewa yanzu haka ya jingine dukkan shirye-shiryen da yake yi na angwancewa da kuma ginin gidansa sakamakon tsadar rayuwar da ake fama da ita. Matashin mazaunin unguwar Darmanawa da ke Jihar Kano yana sana'ar walda ne, inda a da yakan samu N3,000 zuwa N4,000 a kullum, kafin daga baya al'amura su sauya. "Kafin a shiga wannan hauhawan farashi, na sayi fili ina da burin zan gina, har ma na fara tarun kudin bulo da siminti," in ji Musa mai shekara 26. "Yanzu dai halin da na shiga shi ne, komai ya tsaya, idan na samu kudi ma bai huce wanda zan sanya a ajjihu ba. "A yanzu sai na shafe kwana biyu ban samu N2,000 ba saboda babu kwastomomi sosai sakamakon kowa na cikin matsala." Musa ya ce ba shi da wani takamaiman lokaci na ci gaba da shirinsa na gini da aure, amma yana sa ran a kowane lokaci lamurra za su iya daidaituwa. "Ba na tunanin zan iya yin gini a halin yanzu. Ka ga batun sai wani lokacin idan Allah ya kawo dama sai na yi." 'Abin da nake samu yanzu ya daina biya mana buƙata' Shi kuwa Imrana Abdullahi ɗan acaɓa ne a birnin Bauchi da ke arewacin Najeriyar, wanda ya ce wasu miyagu sun sace masa babur ɗin da yake sana'a da shi. Matashin mai shekara 35 ya ce a da yakan samu 1,000 a kowace rana wadda yake ɗan sarrafawa wajen ciyar da matarsa ɗaya da 'ya'ya uku, har ma ya taimaka wa iyayensa. "Ka ga a da idan ka samu N1,000 za ka sayi kwanon shinkafa ɗaya ko ɗaya da rabi, ko kuma ka sayi shinkafa da cefane. Amma yanzu N1,000 ko kwanon shinkafar ba za ta saya maka ba," in ji shi. Imrana ya ce yanzu haka yana amfani da babur ɗin haya ne bisa tsarin ba da bashi. "Dole wani zubin sai mun ƙara lokaci a wajen aikin don a samu a ƙara yawan kuɗin. Wani lokacin kuma ƙarfe 5:00 na yamma ma an samu abin da ake so. "Ga mai ya yi tsada ga gari babu kudi. Rana zafi inuwu ƙuna. Amma mun gode wa Allah da ya ba mu lafiya. Lafiya jarin talaka!"