Menu

Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur

Hoton alama

Fri, 21 Jul 2023 Source: BBC

Masu ababen hawa a Najeriya sun wayi gari ranar Talata da ƙarin farashin man fetur a sassan ƙasar daga kimanin N500 har zuwa naira 640 a kan lita guda.

Ƙarin ya kai kashi 22%.

Matakin dai ya harzuƙa kalamai a shafukan sada zumunta, har ma wasu suna bayyana ɓacin rai.

Ko da yake, babu wata sanarwa a hukumance game da ƙarin farashin man fetur na baya-bayan nan, amma dai Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce lamarin mai yiwuwa yana da alaƙa da tashin farashin man a kasuwar duniya.

A ranar Alhamis da ta wuce, an sayar da gangar ɗanyen man fetur ɗaya a kan kuɗi sama da $80, shi ne farashi mafi tsada da aka sayar da ita tun cikin watan Mayu.

Haka zalika, darajar Naira ta sake yin ƙasa idan an kwatanta da dalar Amurka, kuma ita ma tana da alaƙa da tashin farashin man fetur saboda a yanzu haka ana canzar da $1 a kan N776 a farashin hukuma, sai dai an ba da rahoton cewa an sayar da dalar Amurka har a kan N820 a kasuwar bayan fage.

Kuɗin sufurin man fetur daga defo-defo na Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya zuwa sauran sassan ƙasar, shi ma yana da tasiri wajen ƙara tsadar man, abin da ya sa masu amfani da shi a yankunan arewaci ke sayen man fetur da tsada fiye da na kudanci.

Tuni dai, mutane suka hau dandalin sada zumunta suna bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan al'amari.

A dandalin Fezbuk, Abubakar Ali Ado Bagwai ya koka da cewa ƙarin farashin man ya zo a lokacin da mutane suke cikin mawuyacin hali saboda tsadar rayuwa, musamman ƙarin kuɗin makaranta.

https://www.facebook.com/abubakar.aliado.3/posts/pfbid0ehFFjKaK7U8yCqZti4sqeoUmeMQvXZkdG2HghSvSFgUgUoTYfwF3R5A98jmfvR8Zl?__cft__[0]=AZVUSiBEZ-NIpWvb3vbf_oOdLrFAcC6DMiOFZxpTdJuKLHtBJYVljJwebhvfVgJm5N510KvgGXAH6w2-Gzn-rEsHqXk7U_bI0ps7UV4LtnOlwOGkyFd62u0xeiNXEd3r0vg&__tn__=%2CO%2CP-R

Yayin da Sadiya Datti ke cewa ta kashe sama da naira 46,000 wajen cika tankin motarta bayan an ƙara kuɗin man fetur ɗin.

https://www.facebook.com/sadiya.datti/posts/pfbid0AQFkGoHfbLvi9MK5cdQB12puyAx588hF8BdaqYXyJGSdkUdJXeqw1zjGvsToMdRxl?__cft__[0]=AZVFLbpOX_OXeyrAGp8YyWgB6jB61DYyUFFCyoBF2jTg6fw62cPC0cRMSWtMyMeKdFz6XPl6jZM19RiSW709JEWz4jrTrnpSBOv8hgOcYVeQVr-7AL2apOlj-gxyKYVcKA3ryn7Mwb4hMdqjRqybyxKu&__tn__=%2CO%2CP-R

Isma'eel Abba Tangalashi ya kwatanta halin da aka shiga sanadin ƙarin farashin man fetur ɗin da takurar da Barcelona ta fuskanta a hannun Bayern Munich yayin Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta 2019-2020.

https://www.facebook.com/ismaeel.abba/posts/pfbid0UagLgntnqeRoQoUpop3xXMLemMjAPZH8XP7xzMmL81sPz299NDfmBbMzkm4XtxjYl?__cft__[0]=AZVWUEijUbKm0zWKBOVYlE8Pqv9nsnVt-kQMWygvcH29T0Lj6ud7FmKbe-3IHNeTLVfTQhYTYacrbLojBsbNFBEqtc1nK0LT2AdjsmIuB0Rf3szzrBLNO4W1v-BDm94bOg7MYeDlVwMJNpyISTT65fZU&__tn__=%2CO%2CP-R

Abdullahi Usman Danzomo, da harshen Ingilishi ya rubuta cewa a ganinsa ɓaɓatu kawai a shafukan sada zumunta, ba zai magance matsalar da ƙarin kuɗin man fetur ya haifar ba.

https://www.facebook.com/abdullahiusman.gumel.5/posts/pfbid02HjX2szy154D7cFRgV6LN2pCgHcPPcAFUhrvceEp9oSWZq5WJf9DvFgCqYXRtgQAcl?__cft__[0]=AZUr-zRM98bU7dg0VjxJQUTRjmVTU8jSJ5UzbcsfPlWvmuMDXcWskTADHNCsEnRjl_l9s4O3RHR05gKd-dOB_Ya54uQ_EblmuvXFHdLbvjKSisjhQiXCifn9WhYAnUN6zLYC-Z6VihShOIhG3kZTjqkL1iUqlF_ighYBzMCBqzl5RBmlWUPWAS3Qi2J5MgD4Hzo&__tn__=%2CO%2CP-R

Usman Sadaukhi kuwa addu'a ya yi.

https://www.facebook.com/usman.sadauki/posts/pfbid0qbaAjXrJXzaMufCcvrSVDCDBFeh8Q7Dtty99pe1xtAPVU8S1ZqkZocVSdjjAdc2kl?__cft__[0]=AZVur_6O4tTc3h7sQJNjm7fq2-I1ac_60Qo8bFVTJZ2Usmg7-S0BBFwSQEUOTkPhHniHJEW2DW-zOzH3gMtxw5zVbbkiSLHbz0fW7qlxHAKUH-EI2rRgl3n0nOQ6-d5Y8qcFg96A67w3QakGtIPjQWfpPKyslSW_IuIv8sYwVUC34Q&__tn__=%2CO%2CP-R

Wani ɗan jarida, Nasiru Salisu Zango ya koka ne a kan yadda tashin man fetur ɗin ya zo a lokacin da ake fama da ƙarancin kuɗi da tsadar kayan abinci.

Har yana tambayar shin yanzu da wanne za mu ji?

https://www.facebook.com/mysiro1/posts/pfbid0D1jGDu75F45XHLrrbyvaaSnbg3D2rUPCCmJyDt6Sism5srd4H1VYtAXviQ5w4L6zl?__cft__[0]=AZXd6_fi6cH2GxEKMErHvR65LAGfR32XsvSHNZla3IxAP0DWht660Aa2kNeMl6QOYjjSTAqJ-57ClZm0IMxlzvroUDrljVUrsj7NkXXh4d_dQFfpS8A9MaH2LLE8f-8awEYkWzS5bXs4qkQzdsO4z7ORvXCPZKuyHZjipntq1EfoCQ&__tn__=%2CO%2CP-R

Aliyu Ɗahiru Aliyu ya ɗora alhakin ƙarin kuɗin man fetur a kan ɗumbin basukan da suka yi wa Najeriya katutu da kuma zare hannu da gwamnati ta yi a kan harkar man fetur da canjin kuɗin ƙasashen waje.

https://www.facebook.com/aliyudahiru.aliyu.1/posts/pfbid0M6gFz9wKfH85Bjg4TbR6RiCCi6eUxYwr8fHQHj3dFn7RcjxVvpZk8jdq9je2L1Jkl?__cft__[0]=AZUvs7U_W7ZROxyGa7fAgnTGKyRR8XFXfyylNqMkkwdR9BF_4RwcOnjHPU2p_z-pE2FexIi53ByNPhsGBBdjGc8fbS3vbzcXTpxC26TOke37tV4greiB-ZzlZe4MuRYI_TWLV2r2r3erbjzlB8UXnUuYZtGvlHdmF-RJu3WHtypqUg&__tn__=%2CO%2CP-R

Bashir Ahmad, mai bai wa tsohon shugaban Najeriya shawara kan harkokin sada zumunta ya ce kamata ya yi mutane su fi mayar da hankali yanzu a kan addu'o'in neman Allah ya hore kuɗin sayen mai da sauran kayan buƙatun rayuwa, maimakon ɓaɓatu a kan tashin farashinsa.

https://www.facebook.com/bashahmad/posts/pfbid0XmF6C4kowsivrVxuXqisCYqgctuj8Ee3Cb4NLLD47ZDHfArk9ECH9ZsSh73bUv4yl?__cft__[0]=AZVMukKV7DYJ_hmJJQ2aVexvcuhgyxXGvsA8E96aR7Hi_nP8qQ6Nvm2tzYmy3KjIbbvMDGDWCgCAfFG41jw2GFChNgJoyPw4yi8diwHiSNICvuOal60JEF9q499BruqLfcX_D2OUG5v9nWldScRsLJwVBTNCHBOqdMaeEfuaN0HFvQ&__tn__=%2CO%2CP-R

Bello Bala Shagari ya wallafa da harshen Ingilishi cewa ya cika da mamaki jin cewa mutane ba su fahimci haƙiƙanin yadda rayuwa za ta kasance ba, bayan cire tallafin man fetur. A cewarsa, al'amura za su kasance da tsauri!

https://www.facebook.com/YarimanShagari/posts/pfbid036hmJwYq5FVoeHPzzayVn1fHfeMjcZJwbRyT8Npp4XoES2nFimWr2xtqdrXfUBCswl?__cft__[0]=AZWqw6wCM0pIrT6RAXziMkl24tnBVvk3tf8RvkSFUvJ9Oo5E-XsnWU16nM6WTaPFLfGQ6Bdpfpxio2-0XdX9LcnD3x0WjmLu_EdJ0d0jjzpVdY7zRa6VrlH1yvaeDVIqWcZLVXWu-6m4RDbnqkK93am_sp47MARXcgZY-DWAcPE3rw&__tn__=%2CO%2CP-R

Najeriya, ita ce ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen mai a Afirka amma kuma tana shigar da kashi 90 cikin 100 na man da take buƙata a cikin gida saboda ba ta iya tace man a cikin gida.

Gazawar da ke da alaƙa da durƙushewar matatun man fetur na gwamnati guda huɗu.

A cikin kwana 50 da suka wuce, Shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da matakan tattalin arziƙi da dama ciki har da cire tallafin man fetur da gwamnati ke yi, da dunƙule kasuwar canjin kuɗi duka da nufin daidaita tattalin arziƙin Najeriya da ke cikin mawuyacin hali.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a ranar Litinin ta ba da rahoton cewa alƙaluman hauhawar farashi a watan Yuni sun tashi zuwa kashi 22.79% daga kashi 22.41% a watan Mayu, karo na shida a jere, lamarin da ya haddasa tashin farashin abinci da gidaje da ruwan sha da lantarki da kuma makamashi.

Sai dai, masana tattalin arziƙi a Cibiyar Financial Derivatives Capital sun yi hasashen wani ƙarin hauhawar farashin a wannan wata na Yuli, inda suka nanata cewa a lokacin ne masu sayen kaya za su fara jin tasirin sabbin manufofin tattalin arziƙi don kuwa masu masana'antu da masu shigar da kaya ƙasar suke sake zubi.

Source: BBC