Menu

Kamaru ta ƙaddamar da shirin rage wa talakawa tsadar magani a asibiti

Shugaban Kamaru Paul Biya

Wed, 19 Apr 2023 Source: BBC

Gwamnatin Kamaru za ta fara aiwatar da shirin kula da lafiya na bai-ɗaya, don rage wa 'yan ƙasar miliyan shida tsadar magani da sauran kuɗin da ake kashewa a asibiti.

Shirin dai na haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da abokan ƙawancen Kamaru na duniya kan ayyukan ci gaban ƙasa. Ana sa rai tallafin kula da lafiyar zai ɗauke wa marasa lafiya nauyin kusan kashi casa’in da biyar cikin ɗari na kuɗaɗen asibiti.

Mata masu juna biyu da ƙananan yara ne za su fara cin gajiyar wannan shirin a zagayen farko.

Tsarin kula da lafiya na bai-ɗaya wanda a karon farko ake ƙaddamar da shi a Kamaru, wata dama ce da hukumomi suka tanada, don sauƙaƙa wa masu ƙaramin ƙarfi, da masu fama da wasu nau'o'in cutuka damar samun ayyukan kula da lafiya cikin sauƙi.

Kashi mafi yawa na kuɗaɗen da za a zuba cikin shirin, zai rataye ne a wuyan gwamnatin Kamaru.

Ministan lafiya na Kamaru, Manaouda Malachie ya ce shirin zai ba da damar kyautata kula da marasa lafiya, abin da zai ƙara yawan masu zuwa asibiti don bincika lafiyarsu.

Ministan ya ce "kamar yadda kuka sani akwai wani kaso na jama’a da ba sa iya zuwa asibiti dalilin rashin kuɗi, amma yanzu za a samu sauƙi, don ba lallai ne mutum ya biya abin da ake nema daga gare shi, kai tsaye ko nan take ba".

Ya kuma ce: "Sai dai tsarin da za a gudanar a zagayen farko zai ƙunshi larduna biyar na ƙasar cikin goman da ake da su".

Manaouda Malachie ya kuma ce za a kashe jimillar kuɗi saifa miliyan ɗari ba goma wajen kula waɗanda za su ci gajiyar tsarin a asibitoci ta hanyar samun alluran riga-kafi da ciyarwa da samun kulawa ga majinyaci da wasu cutukan da suka fi addabar jama’a.

Su wane ne za su ci gajiyar shirin?

Ɗaya daga cikin matan da suka fara cin moriyar shirin ta shaida wa BBC cewa gaskiya za a samu canji da yawa wajen kula da lafiya.

Ta ce: "Saboda kuɗi ƙalilan maras lafiya zai kashe don haka ko mutum a bayan gari yake, ba zai samu wata damuwa ko tsaiko kafin a duba lafiyarsa ba".

A cewar Minista Manaouda Malachie, mutanen da za su fi cin gajiyar shirin su ne mata masu juna biyu, da ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar, da masu ciwon ƙoda da ke zuwa asibitoci don tace jini, da masu kurkunu da masu cutamai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs.

Haka kuma a cewar ministan, illahirin 'yan ƙasashen waje mazauna Kamaru su ma za su amfana a ƙarƙashin wannan shirin kula da lafiya.

Masu fama da ciwon koda, da ke zuwa asibiti don tace jini suna biyan kuɗin da ya kai jaka 750 ne a shekara, amma a ƙarƙashin sabon shirin za su riƙa biyan jaka 15 ne kacal a shekara.

Ana buƙatar duk wanda ya cika sharuɗɗan da aka gindaya na shiga cikin shirin, sai ya fara yin rajista.

Source: BBC