BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kante ya amince zai koma Al-Ittihad

Ngolo Kante

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Ɗan wasan Faransa mai taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea N'Golo Kante ya amince ya koma ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya da taka leda.

Dama dai a wannan wata na Yuni ne kwantaragin Kante ke ƙarewa a Chelsea.

A baya-bayan nan ɗan wasan na tsakiya ya yi ta fama da rauni, inda ya buga wa Chelsea wasa sau tara kacal a kakar wasa ta 2022/2023.

Kante ya bi sahun ƴan wasa ƴan uwansa kamar Karim Benzema wanda shi ma ya koma Al-Ittihad daga Real Madrid.

A lokacin zamansa a Chelsea, Kante na cikin ƴan wasan da suka taimaka kungiyar wajen lashe kofin zakarun Turai na Champions League, da firimiya na Ingila, da Europa da kuma kofin FA.

Gabanin komawarsa Chelsea, ya taimaka wa Leicester City ta samu lashe kofin firimiya a kakar wasa ta 2015-16.

A yanzu ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara 3 da ƙungiyar ta Al-Ittihad kan kuɗi fam miliyan 86.

Source: BBC