Chelsea da Leicester za su kece reni a ranar Asabar, a wasan karshe na kofin kalubale da za a yi a filin wasa na Wembley da ke birnin London.
Chelsea ta lashe kofin kalubale wato FA sau takwas a tarihi, kuma Tottenham ce kawai ta taba kafa irin wannan tarihi.
A bangare daya kuwa Leicester City ba taba cin kofin ba, sai dai ta taba zuwa wasan karshe a shekarar 1969 inda ta yi rashin nasara a hannun Manchester City 1-0.
A wasanni shida da a ka buga a baya tsakanin kungiyoyin biyu Chelsea ba ta yi nasara ko da sau daya ba, inda tayi rashin nasara biyu, canjaras hudu.
Wasan da suka buga na Lig a watan Janairu Leicester ce ta doke Chelsea 2-0 a filin wasa na King Power, wanda ya zama na karshe ga tsohon mai horar da kungiyar wato Frank Lampard.
A duka kungiyoyin da suka taba lashe kofin Premier League, Leicester ce kawai ba ta taba cin kofin kalubale na FA ba.
To amma kuma kamar yadda tarihi ya nuna mai horar da kungiyar Brendan Rodgers bai taba rashin nasara a filin Wembley ba a wasanni karshe da ya je da wasu kungiyoyin sau shida.
A karon farko yan kallo 20,000 ne za su kalli wasan da za a yi a filin Wembley da ke London, kuma hukumomi sun dauki wannan mataki ne lura da saukin da lamurra suka yi kan abinda ya shafi bazuwar annobar Korona.