Manchester United ta kai zagayen karshe a FA Cup na bana, bayan da ta ci Brighton a bugun fenariti ranar Lahadi a Wembley.
United ta kai karawar karshe da cin 7-6 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da suka tashi 0-0.
Ranar 3 ga watan Yuni za a buga wasan karshe tsakanin Manchester City da Manchester United a Wembley.
United wadda ke taka rawar gani a kakar nan ta lashe Carabao Cup a bana, bayan da ta ci Newcastle.
Kungiyar Old Trafford mai kwantan wasa biyu tana ta hudu a kan teburin Premier League na bana.
Karo na uku a tarihin United da ta kai zagayen karshe a kofi biyu na cikin gida da ta yi wannan kwazon.
Na karshe da ta yi wannan kokarin shine a 1993/94 karkashin Sir Alex Ferguson, wanda ya ci Chelsea 4-0 a FA Cup a wasan karshe a Wembley.
A kakar ce United ta lashe Premier League, amma ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa 3-1 a League Cup.
A kakar 1982/83 United ta je wasan karshe a Wembley, inda ta fuskanci Liverpool a lokacin ana kiran gasar da Milk Cup a lokacin Atkinson ne kociyan United.
A FA Cup kuwa a kakar United ta yi nasara a kan Brighton da ci 4-0.
Kawo yanzu United ba ta taba lashe FA Cup da League Cup ba a kaka daya, amma Arsenal ce ta daya da ta fara hakan a 1992/93.
Gunners ta yi nasarar doke Sheffield Wednesday a FA Cup da League Cup a kakar.
Sai dai Liverpool ta yi haka karo biyu, wadda ta caskara Chelsea a FA da League Cup, itama Manchester City ta yi wannan bajintar.
Arsenal ce kan gaba a yawan lashe FA Cup 14, wadda ta je wasan karshe 21, kamar yadda United keda shi idan ka hada da na bana mai kofi 12.
Ranar 3 ga watan Yuni Erik ten Hag na fatan zama koci na farko da zai lashe kofin cikin gida biyu a kaka daya a Manchester United.