Kasashen yammacin duniya da dama sun sanya wa jami'an China takunkumi a kan cin zarafi da take hakkin tsiraru 'yan kabilar Uighur, wadanda yawancinsu Musulmi ne.
Gwanatin China ta tsare 'yan kabilar Uighur ne a sansanoni na musamman a yankin arewa maso yamma na Xinjiang, inda ake zargin ana gana musu azaba da sa su aikin dole da sauran nau'ukan cin zarafi.
China ta musanta zarge-zargen da cewa sansanoni ne na bayar da tarbiyya don yaki da akidar tsattsauran ra'ayi, da koyar da sana'o'in hannu.
Kasashen na yammacin duniya sun dauki matakin sanya wa China takunkumin ne a wani tsari da kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka da kuma Canada suka yi.
Takunkumin da ya hada da na hana tafiye-tafiye da dakatar da kadara, ya shafi manyan jami'an gwamnatin China ne a yankin na Xinjiang, wadanda ake zargi da take hakkin Musulmin 'yan kabilar Uighur.
To sai dai Chinar kamar a ko da yaushe ta musanta dukkanin zargin da ake yi mata na cin zarafin Musumin, tana cewa sansanonin da ta ajiye su, wurare ne na sake musu tarbiya don raba su da tsattsauran ra'ayi,
Haka kuma ta mayar da martini da irin nata takunkumin a kan jami'an kasashen Turai.
A kalamansa kan daukar matakin hukunta jami'an na China ta hanyar sanya musu takunkumi, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Dominic Raab, ya ce, abin da ake yi wa Musulman 'yan Uighur tsabar take hakkin dana dam ne.
Mista Raab ya ce cin zarafin nasu a Xinjiang na daya daga cikin take hakkin bil adama mafi muni a wannan zamani.
Rabon da kungiyar Tarayyar Turai ta sanya wa China sabbin takunkumi a kan take hakkin dan adam tun 1989 a lokacin yamutsin dandalin Tiananmen Square, lokacin da jami'an tsaro a Beijing suka bude wuta a kan masu zanga-zangar tabbatar da dumokuradiyya.
A wata sanarwa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya ce China na aikata laifukan kisan kiyashi da cin zarafin dan adam.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Canada a wata sanarwa da ta fitar dangane da lamarin , cewa ta yi, tarin shedar da ake samu na nuna yadda hukumomin China ke take hakkin dan adam.
An dauki matakin sanya takunkumin ne yayin da kasashen duniya ke kara sanya ido da bincike a kan yadda Chinar ke yi wa Musulmin 'yan Uighur.
An yi kiyasin akwai sama da 'yan Uighur miliyan daya da sauran tsirarun kabilu da ake tsare da su a sansanonin na China.
Ana zargin gwamnatin kasar da tilasta yi wa matan Musulman aikin hana su haihuwa da kuma raba 'ya'ya da iyayensu.
Gwamnatin China ta hana tashar talabijin ta BBC daukowa da kuma yada rahotanni kan batun na 'yan kabilar Uighur da kuma na cutar korona.