0
MenuAfrica
BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Pedri, Suarez, Neves, Ronaldo, Mbappe da Ibrahimovic

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Dan wasan gaban Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai iya tafiya Paris St-Germain idan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya zabi tafiya Real Madrid. (Tuttosport, via Mirror)

Kazalika Real Madrid na kallon kanta a matsayin wace ke kan gaba a yunkurin daukar Mbappe a bazara. (AS)

Liverpool ta bayyana aniyarta ta daukar dan wasan tsakiyar Barcelona Pedri, abin da ya sa Barca ta nemi sabunta kwangilar dan wasan na Sifaniya mai shekara 18 da karin kudi da ya kai kusan £350m. (Sunday Mirror)

Ana hasasen cewa dan wasan gaban Atletico Madrid Luis Suarez zai koma Liverpool, shekara bakwai bayan dan kasar ta Uruguay ya bar kungiyar. Kazalika ana rade-radin cewa zai tafi kungiyar Inter Miami ta David Beckham. (Todofichajes, via Sun on Sunday)

Dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 27, zai matsa lamba domin ganin ya bar Tottenham a bazara idan kungiyar ta gaza samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kakar wasa mai zuwa. (Athletic - subscription required)

Manchester United ta kara dan wasan tsakiyar Wolves Ruben Neves, mai shekara 24, a cikin jerin 'yan wasan da take son dauka, yayin da Wolves ta shirya sayar da dan kasar Portugal din. (90min)

Ana rade radin cewa dan wasan gaban Everton da Italiya Moise Kean, mai shekara 21, wanda ke zaman aro a Paris St-Germain, zai koma Juventus. (Tuttosport - in Italian)

Manchester United da Leeds sun bi sahun wasu kungiyoyi a yunkurin daukar dan wasa mai shekara 18 Kyron Gordon daga Sheffield United. Kazalika ana alakanta Everton da Liverpool da yunkurin daukar matashin dan wasan na Ingila. (Mail on Sunday)

Newcastle United na saya ido kan dan wasan Wolves mai shekara 21 dan kasar Ingila Dion Sanderson, wanda yake zaman aro a Sunderland. (Chronicle)

Arsenal ta tuntubi dan wasan Fluminense da Brazil mai shekara 19 Matheus Martinelli, wanda Manchester United ke son dauka. (Globo Esporte, via Football London)

Kocin Everton Carlo Ancelotti ya mayar da hankali wajen daukar dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, a yayin da dan wasan Colombia Yerry Mina, mai shekara 26, yake son barin kungiyar. (Tuttomercatoweb, via Mail on Sunday)

Dan wasan gaban Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 39, yana "dab da kammala" kulla sabuwar yarjejeniya da AC Milan, a cewar Paolo Maldini. (Sky Italia - in Italian)

Source: bbc.com