BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kazuyoshi Miura: Dan shekaru 55 da har yanzu ke buga kwallo

Kazuyoshi Miura

Wed, 1 Feb 2023 Source: BBC

Kazuyoshi Miura na dab da bikin zagayowar haihuwarsa, inda zai cika shekara 56 a duniya.

To amma har yanzu jikinsa bai nuna cewa ya gundura da buga kwallon kafa ba.

Dattijon na harin cika shekara 50 a matsayin kwararren dan kwallo, kuma a yanzu ma ya kulla yarjejeniya da kungiyar Oliveirense ta Portugal don ci gaba da taka leda.

Ya tafi kungiyar ne zaman aro daga Yokohama FC ta kasarsa Japan.

Zuwansa Portugal na nufin ya buga wasa a kasashen duniya shida, da suka hada da Brazil, Japan, Italy, Croatia da kuma Australia.

'' Duk da nan sabon wuri ne gare ni, zan yi aiki tukuru don in nuna wa duniya salon wasan da aka sanni da shi,'' in ji Miura.

A baya ya fadi cewa yana da burin ci gaba da wasa har sai ya kai shekaru 60.

Miura ya fara wasansa a Santos a 1986, kuma ya zama dan wasa mafi tsufa da ya taba cin kwallo a gasar kwararru ta Japan, inda ya ci kwallo a 2017 yana da shekaru 50 da kwana 14.

Ana masa kirari da ''King Kazu'' a Japan, sannan ana girmama shi a matsayin daya daga cikin sanannun fuskoki a fagen wasannin kasar.

Hotonsa Kazuyoshi Miura ne madubin J League, a lokacin da aka kaddamar da shi a 1993.

Ya ci wa Japan kwallo 55 a wasanni 89 da ya buga mata.

Source: BBC