BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kenya za ta haramta kai daliban karamar sakandare makarantar kwana

Kenya School Stampede 8903 Hoton alama

Wed, 7 Dec 2022 Source: BBC

Kenya na shirin soke makarantar kwana ga daliban da ke matakin karamar sakandare da firamare, ga 'yan kasa da shekara 15, kuma haramcin zai fara aiki a shekara mai zuwa.

Sakataren ilimi na Kenya, Belio Kipsang ya shaida wa zauren babban taron malaman makaranta da ake yi cewa, iyaye za su ci gaba da kai 'ya'yansu makarantun jeka da wo kafin su kai matakin babbar sakandare ko kuma cika shekarun da ya dace.

Ya kara da cewa gwamnati, ta dauki matakin ne domin bai wa yara damar zama tare da iyayensu, da koyar da su tarbiyya mai kyau.

Sai dai dalian da suka fito daga yankunan karkara wannan doka ba za ta shafe su ba.

Kashi 28 cikin 100 na makarantun firamare a Kenya na bin tsarin makarantun kwana, kuma sakataren ilimi Belio ya ce adadin ya yi yawa idan aka kwatanta da wasu makarantun na kasashe.

''Hakki ya rataya a wuyan iyaye na kula da yaransum da ba su tarbiyya, da koyar da su ilimi matakin farko, ba za mu amince a kwace ragamar tarbiyya da iyaye ya kamata su yi ga malaman makarantu ba.

Lokaci ya yi da ya kamata mu gane nauyi da hakkin da ya rataya a wuyanmu, mu san yaran nan na bukatarmu, kuma ita ce hanyar da za mu shakuwa da su idan su na makarantar jeka dawo,” in ji shi.

Source: BBC