BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Klopp ya ce bai da niyar barin Liverpool nan kusa

94331739 Kocin Liverpool Jurgen Klopp

Tue, 17 Jan 2023 Source: BBC

Jurgen Klopp ya ce ba zai bar Liverpool ba sai iidan an kore shi, ya kuma yi karin haske kan canje-canje da zai yi a Anfield.

Ya yi wannan kalaman bayan kasa taka rawar gani da Liverpool ke yi, wadda take ta tara a teburin Premier League.

Haka kuma an bai wa kungiyar Anfield tazarar maki 10 a gurbin 'yan hudun farko a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

''Sai dai idan an samu sauyi daga shugabancin kungiyar ko kuma wani gagarumin abu ya faru da ke bukatar canji'' in ji Klopp.

''Kawo yanzu kamar yadda na sani, sai wani ya bukaci da na bar kungiyar, amma yanzu ina nan daram.''

Ya kara da cewar ''Hakan na nufin cewar mun kai lokacin da za mu sauya wasu abubuwan. Za kuma mu duba hakan, amma hakan sai nan gaba, zuwa karshen kakar nan. Amma ba a wannan lokacin ba.''

''Ina da lokacin da zan yi tunani sosai, Ya kamata mu kara kwazo fiye da yadda muke a yanzu.''

Klopp ya ce da kyar ne idan za su kara cefane, bayan daukar dan kwallon Netherlands, Cody Gakpo a Janairu, yayin da 'yan wasa hudu kwantiraginsu zai kare a karshen kakar nan.

'Yan wasan sun hada da James Milner da Naby Keita da Alex Oxlade-Chamberlain da kuma Roberto Firmino.

Ranar Asabar Brighton ta ci Liverpool 3-0 a gasar Premier League, daya daga karawar da kungiyar Anfield ta yi mai muni a tarihi da ta kasa yin abin kwazo.

Liverpool za ta kara da Wolves ranar Talata a wasan zagaye na uku a FA Cup.

Source: BBC