BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ko Tottenham za ta kai zagayen gaba a Champions League?

69842348 Yan wasan Tottenham cikin murna

Wed, 12 Oct 2022 Source: BBC

Tottenham za ta karbi bakuncin Eintracht Frankfurt, domin buga wasa na hudu a rukuni na hudu a Champions League. A makon jiya Frankfurt da Tottenham suka tashi 0-0 a wasa na uku a cikin rukuni a Jamus. Sporting ce ta daya a rukuni na hudu da maki shida, sai Tottenham da Frankfurt da kowacce keda maki hurhudu. Kungiyar da Antonio Conte ke jan ragama za ta buga karawa ta hudu a cikin watan Oktoba daga fafatawa taran da za ta yi. Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Arsenal a Premier League da ci 3-1 da tashi 0-0 da Frankfurt a Champions League, sai ta ci Brighton 1-0 a Premier a Oktoban. To sai dai Dejan Kuluseski ba zai yi wa Tottenham wasan ba, sakamakon jinya da yake yi, amma Lucas Moura ya murmure. Kulusevski ya ji rauni a lokacin da yake yi wa Sweden tamaula a watan jiya, amma ya kusan komawa atisaye. Rabon da Moura ya buga wa Tottenham tamaula tun cikin watan Agusta, wanda ake sa ran zai fara da zaman benci a wasa da kungiyar Jamus. Dan wasan Tottenham Harry Kane, ya ci kwallo takwas a wasa tara a Premier League ta bana, amma bai zura kwallo ba a raga a Champions League tun fara kakar 2022/23.

Source: BBC