BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ko akwai bukatar a riƙa tantance malamai kafin su fara wa'azi?

Wasu Malaman Musulunci

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya na ci gaba da taƙaddama kan kalaman wani malami addinin Musulunci da ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.

Mutane da yawa sun yi zargin cewa kalaman Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi game da matsayin Annabi Muhammadu sun yi kaushi kuma ba su dace ba.

Cikin masu mayar da martani har da malaman addinin Musulunci daga ɓangarori daban-daban.

Lamarin har ya kai ga muhawara a kan ko ya kamata gwamnati ta riƙa tantance malaman da ke wa'azi a faɗin ƙasar ko a'a.

BBC ta tuntuɓi malamai da dama a Najeriya kan wannan batu, kuma sun bayyana ra'ayoyi mabambanta.

Akasari bakin malamai ya zo ɗaya

Sheikh Noor Khalid, fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce "irin wannan matsala ta wa'azi ce ta kai ƙasar ga yaƙin Malam Muhammadu Marwa wanda aka fi sani da Mai Tatsine.

"Irin wannan damar wa'azin barkatai ce ta kai ga rikicin Boko Haram, kuma shi ne ya kai ga rikicin Abduljabbar Nasiru Kabara," in ji Malam Nooru Khalid.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar "samar da hukumar da za ta riƙa tantance malamai don tabbatar da ganin sai mutumin da ya cancanta ne za a bai wa damar yin wa'azi".

Irin wannan ra'ayin ne da Malam Ibrahim Kabiru Mai Ashafa, wanda shi ma wani babban Malamin addini ne a Najeriya.

"Ilimi daban damar yin wa'azi daban, tsantsar karatu ba ya nufin mutum ya kai ya fara hawa mumbari don yin karatu ga al'umma.

"Tun lokacin sahabbai Abdullahi bin Mas'ud ya ce, 'Masu ilimi sun yi yawa a wannan lokaci, amma waɗanda za su hau mumbari su yi wa'azi, sun yi ƙaranci ƙwarai da gaske," in ji Malam.

Ya ce a zamanin sahabban ga yawan masu ilimi amma ba yawan masu wa'azi, mu kuma ga ƙarancin masu ilimi amma ga yawan masu wa'azi.

Malam Aminu Ibrahim Daurawa cewa ya yi wannan daɗaɗɗen ra'ayinsa ne, "gwamnatoci da ƙungiyoyi da ɗariƙu su zo, a samar da wani kwamitin malamai kan yadda za a riƙa tantance masu wa'azi da kuma sigar yadda za a riƙa yin wa'azin.

"Ya zama cewa wanda ba shi da lasisin wa'azi ko kuma ba ya bin sharuɗɗan da aka gindaya, ba zai ci gaba da wa'azi ba," in ji Malam Daurawa.

Su wane ne za su riƙa tantance masu wa'azin?

Wata gagarumar matsala da za a iya fuskanta, wadda ga alama za ta fi kafa kwamitin wahala, ita ce ɓangaren da zai tantance malaman.

Ganin cewa a Najeriya akwai ɓangarori daban-daban na mabiya addinin Musulunci.

Malam Nooru Khalid ya ce ƙasashe irin su Saudiyya da wasu a Gabas ta Tsakiya, suna da irin wannan kwamitin da ke tantance masu wa'azi, abin da ya sa da wuya ka ji suna fuskantar irin wannan matsalolin na ruɗun addini.

"Ba kwamitin ba ne ke faɗa wa malami abin da zai koyar, a'a mafi yawan lokuta cewa ake yi babu ruwanka da wa'azi a kan kaza da kaza," in ji Shiek Nooru.

Malam Daurawa cewa ya yi, "bangarorin baki ɗaya za su kawo wakilai ne sannan gwamnati ta kawo nata da ta aminta da su, a je jami'o'i a ɗauko masana daga fanni daban-daban su zama suna cikin wannan kwamiti".

A tarihin malaman Bagadaza sun taɓa hana wani babban malami mai suna Ibni Shambooz wa'azi saboda abubuwan da yake yi, sun sha bamban da koyawar da ake fatan al'umma su zauna a kai.

"Malaman Bagadaza cewa suka yi, ya haramta ya riƙa koyarwa, ga shi kuma babban malami ne, saboda a karatun nasa babu tarbiyya ciki," in Malam Mai Ashafa.

Kalubalen kafa kwamitin a Najeriya

Ga irin su Malam Aminu Daurawa da suka yi yunƙurun kafa irin wannan kwamiti lokacin da ya jagoranci hukumar Hizba ta jihar Kano a baya sun fuskanci ƙalubale mai yawa.

"Ni so na yi a ce har waƙar da muke yi ta yabon Manzon Allah ko wani malami ko shehi ya zama ana tantance su, idan sun ci karo da koyarwar addini a cewa mai ita ya je ya gyara.

"Idan kuma wasu kalamai ne aka yi a ciki marasa daɗi da za su iya haifar da ruɗu ko rikici sai a tilasta masa ya janye su, ko ya cire su, ko kuma ya gyara su," in ji Daurawa.

Ganin cewa Najeriya na da mabambantan addinai da kuma mabiya a cikin kowanne addini zai yi wuya a iya samun abin da ake so.

Siyasa

Masana na ganin cewa ko an kafa irin wannan kwamiti, 'yan siyasa za su iya taka rawa wajen ganin sai malamin da suke da ra'ayi ne za a bai wa lasisi ko a hana shi.

Idan ya kasance ɗan siyasa na ɗasawa da malami musamman zai tabbatar da sunan malamin ya shiga cikin jerin waɗanda za su samu lasisin.

Akasin haka sai dai malamin ya riƙa koyar da iyalansa.

"Idan kuna da ra'ayin siyasa hakan zai iya tasiri kan samun lasisin ko rashin samu," in ji Malam Aminu Daurawa.

Tsarin Mulki

Wasu masana na kallon tsarin mulki a matsayin tarnaƙi ga yunƙurin kafa irin wannan kwamiti.

Ganin cewa ya bai wa duk wani ɗan ƙasar 'yancin faɗar albarkacin bakinsa, sai kuma a ce malamai ne kawai za a hana faɗar nasu.

"Wannan wata matsala ce da za a fuskanta daga masu wa'azi a manyan addinan biyu.

Musulunci da Kiristanci, don haka sai dai idan jiha ce ke son yin haka a matakinta na jiha tun da tana da wannan 'yanci," kamar yadda Malam Daurawa ya yi ƙarin bayani.

Rikicin cikin gida na ƙungiyoyin addinai

Wannan ya fi alaƙa da rikici tsakanin malaman da kansu.

Misali cikin mabiya Izala sun kasu biyu, mabiya bayan wannan malamin da na wannan idan baka goyon bayan wannan, sai ya nemi a ƙi ba da sunanka.

Haka abin zai iya kasancewa a ɓangaren ɗariƙu, idan baka faira wataƙila a hana ka damar da za ka wakilci Tijjaniya.

Ko kuma baki ɗaya Ahalussuna da suka haɗa da ɗariku da Izala su juya baya ga malamai mabiya mazhabar shi'a, saboda saɓanin fahimta ko banbancin ra'ayi.

Najeriya dai na fuskantar matsaloli masu alaƙa da addini, kuma da yawan gwamnatoci da ɗaiɗaikun mutane na fargabar tsoma baki kan irin wannan sha'ani a duk lokacin da ya taso.

Sai dai wata matsala da ta sake kunno kai ta wani bangare ita ce, kafafen sada zumunta (Social Media) da su jama'a da dama sun zama malamai masu wa'azi.

Wasu kuma sun zama 'yan jarida masu watsa labarai, yayin da wasu kuma suka zama masu sayar da magani a irin waɗannan dandali.

Source: BBC