A yayin da Hong Kong ke shirin bayar tikitin jirgi 500,000 kyauta domin kara jan hankulan 'yan yawon bude idanu su koma yankin, wanda annobar cutar Korona ta yi wa illa, mutanen da ke aiki a hukumomin yawun bude ido da na jin dadi da walwalar jama'a na kasar na ci gaba da mayar da martani game da matakin. Shin bayar da kyautar tikitin jirgi na kusan dala miliyan 255 ka iya dawo da walwala a kasar, duk kuwa da tsauraran dokokin kullen Korona da kasar ke da su? Paul Chan - wani dan kasuwa ne da ke aiki a wani kamfani da ke kula da masu yawon shakatawa - ya ce suna maraba da duk wani mataki da zai kawo wa kasar bunkasa ta fannin tattalin arziki. 'Ya kamata matakin ya zarta haka' Paul ya fada cikin murmushi cewa ''Bayar da kyautar tikitin jirgi domin janyo hankalin masu yawon shakatawa kwakkyawan mataki ne''. ''To amma ina son sanin su wa za a bai wa kyautar tikitin, idan kamfanonin jirage sun amince, sannan kuma mutanen suka shigo kasar, za su dauki lokaci a nan kasar to......'' Sai mista Paul ya fasa bayyana mana aihinin abin da yake son fada. Hukumar da ke kula da filin jirgin sama na Hong Kong din ta ce za a bayar da tikitin ne kawai ga kamfanonin jiragen sama na cikin gida. Wadanda suka hadar da Hong Kong Express da Hong Kong Airlines - wadanda mafi yawancinsu ke zirga-zirga zuwa China, da Japan da kuma kudu maso gabashin Asiya - tare da kamfanin jirgin sama na Cathay Pacific, wanda ke zirga-zirga a fadin duniya. Ta kara da cewa tana bin tsarin da aka bayyana tun farkon annobar, na ci gaba da bayar da tikiti ga 'yan kasar da na kasashen waje, idan annobar ta kare. Kamfanin su Paul ne ke tanadar wa da masu yawon shakatawa 'yan kasashen waje da 'yan kasa kayayyakin na al'adun kasar masu daukar hankalin 'yan yawon bude idon. "Mun fara a 2013 kuma harkoki suna tafiya daidai kafin barkewar annobar Korona. Daga nan kuma abubuwa suka tsaya cak! Dan haka dole mu samar wa kanmu mafita domin samun kudade, a maimakon jiran 'yan yawon bude ido daga kasashen waje. Ya ce dole suka mayar da hankali ga 'yan kasar ta hanyar shirya musu tafiye-tafiyen neman ilimi bayan da dokokin kullen korona suka sauya komai. ''Da haka muka samu yadda muka tafiyar da al'amura. Dan haka yanzu ina fatan wannan kyautar tikiti zai taimaka wajen bunkasa harkokin yawon bude ido tare sauran harkokin kasuwanci a cikin yankinmu''. Ya kuma bayyana damuwarsa kan tsadar sauran bangarorin yawon bude idon, ba tsadar kudin jirgi ne kadai abin dubawa ba. Kafin annobar Korona kwastomominmu na kashe makudan kudi domin yawon shakatawa. dan haka ya kamata a yi sassauci kan kudin da suke biya domin yawon shakatawar, ba kudin jirgi kadai ba, tun da so ake a inganta harkar yawon shakatawar''. Kawo karshen killacewa Yankin Hong Kong shi ne yankin da ya fi tsauraran dokokin korona a fadin duniya cikin fiye da shekara biyu, to amma a yanzu birnin ya fara sassauta dokokin. Ranar 23 ga watan Satumba kasar ta kawo karshen dokar killace mutanen da suka shigo kasar wadanda gwaji ya nuna cewa basa dauke da cutar. Moon Tsui wata mai shirya taruka da wasanni ce ga masu yawon bude ido, ta kuma ce tana maraba da duk wani mataki da zai taimaka wajen janyo hankalin masu yawon bude ido zuwa cikin kasar. ''Abubuwa sun tsaya min cak! fiye da shekara biyu. To amma tun cikin watan Yuni aka fara kirana ana neman na shirya taruka. Kuma duk mutanen da ke neman na shirya tarukan suna fada min ranaku da yadda suke son tarukan nasu, dan haka ina jin komai ya kusa kankama. ''Na tabbata kyautar tikitin za ta ja hankalin mutane masu yawa''. Moon ta yi maraba da kawo karshen dokokin Korona. ''Abu mai matukar muhimmanci shi ne sauyi game da dokokin killacewa, kafin yanzu, duka mutanen da suka shigo kasarmu su kan kwashe wasu makonni killace a Hotel''. "Abubuwan da ke tafe nan gaba a kasar kamar kwallon zari ruga da taron zuba jari sune ma'aunan da za ayi amfani da su domin ganin ko har yanzu Hong Kong na nan a matsayinta na kasar yawon bude idanu''. Martanin kamfanonin tafiye-tafiye Ya ya sauran kamfanonin shirya zirga-zirga suka ji da matakin bayar da kyautar tikiti 500,000? Ma'aikatar kula da harkokin yawon bude ido ta kasar ta ce tsakanin shekarar 2013 zuwa 2019 kasar na karbar bakuncin mutum miliyan 58 a duk shekara. Amma a wata taran farkon wannan shekarar mutum 249,699 ne kawai suka je kasar. Bayan jin wannan labari Frankie Chow, mamallakin kamfanin shirya tafiye-tafiye na Ulu Travel, ya shaida wa BBC cewa, ''Muna matukar marabara da mutanen da za su shigo, saboda mun dauki shekara uku muna jiran wannan rana. Lokaci ne mai matukar tsauri a garemu. Masu gidajen abinci Nicolas Elalouf, wani wanda ke tafiyar da wani gidan abinci a yankin da 'yan yawon bude ido ke yawan ziyarta, ya ce matakin abun ya yaba ne. "A ranar Juma'a ne aka dakatar da dokar killacewa, kuma a wannan ranar ne da daddare na fara shirya gidan abincina''. Ya ci gaba da cewa mafiya yawan kwastomominsa 'yan yawon bude ido ne, dan haka a ganinsa wannan matakin abin a yaba ne. To amma ya bayyana damuwarsa game da cewa kyautar tikitin jirgi kadai bai wadatar ba. ''Idan aka samu karin barkewar cutar, a wanna kasa mai tsauraran dokoki, me kake tunanin zai faru? Idan mutane suka zo kyauta kuma ka ce sai an killacesu kenan matakin ba shi da wata fa'ida'' 'Mataki ne mai kyau' John Prymmer wani mai gidan rawa ne a yankin. an tilasta masa bin dokokin korona na rufe gidajen rawa da na shirya taruka a yankin. John ya ce bayar da kyautar tikitin jirgi kadai ba zai taimaka wa fannin yawon shakatawa ba. "Mataki ne mai kyau, musamman ta bangaren gwamnati'' John ya ci gaba da cewa ka'idar da aka saka ta gwajin cutar korona bayan shiga kasar ka iya kawo wa matakin cikas. Bayan fama da kwastomomin cikin gida da ya yi a karshen mako a yanzu Paul Chan, na cike da fatan cewa fannin yawon bude ido zai farfado. "Karuwar farashin makamashi da ci gaba da yake-yake ka iya kawo ya duniya tabarbarewar tattalin arziki, wanda kuma hakan ka iya shafar fannin yawon bude ido, dan haka ban sani ba ko kyautar tikitin jirgi ka iya bunkasa fannin''. Kuma bayar da kyautar tikiti rabin miliyan domin dawo da harkokin yawon bude ido a kasar, alama ce da ke nuna hukumomin kasar a shirye suke domin shiga sabon babin bunkasa fannin.