Menu

Ko farashin man fetur zai iya sauka a Najeriya?

Hoton alama

Wed, 19 Jul 2023 Source: BBC

A ranar Talata, ba zato babu tsammani ƴan Najeriya suka tashi da labarin ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar.

Farashin litar man fetur ya kai naira 617 a sassan ƙasar, ƙari a kan 540 da aka saba sayarwa a baya.

A jawabinsa na karɓar mulki, shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya ingiza farashin litar man daga kimanin naira 200 zuwa naira 600.

Cire tallafin man fetur dai na nufin za a riƙa samun hawa da saukar farashin litar mai domin kuwa kasuwa ce za ta tantance farashin.

Kuma hakan na nufin ƴan kasuwa za su iya shigar da man fetur daga ƙasashen waje kuma su sayar a farashin da suke so ta yadda za su mayar da uwar kuɗi kuma su samu riba.

Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin farashin sufuri da kayan masarufi ya riƙa hauhawa.

Lamarin da ya sanya gwamnatin ƙasar ta ce za ta fito da wasu shirye-shiryen da za su sauƙaƙa wa mutane raɗaɗin cire tallafin.

Yaya farashin man fetur ke ƙaruwa a Najeriya?

Najeriya na shigo da sama da kashi 90 cikin ɗari na man fetur da ƴan ƙasar ke amfani da shi a kullum saboda gazawar ta wajen tace nata ɗanyen man.

Hakan na faruwa ne duk da cewa Najeriyar ce kan gaba wajen fitar da ɗanyen man fetur a Afirka.

Dukkanin matatun man fetur na ƙasar sun durƙushe, yayin da har yanzu matatar man fetur mai zaman kanta ɗaya tilo (Ɗangote) da aka gina ba ta fara aiki ba.

Tunda Najeriya na shigar da man fetur ɗin da take amfani da shi ne daga waje, to kuwa farashin litar man za ta riƙa sauyawa daidai da sauyawar farashin gangar ɗanyen man fetur a kasuwar duniya da kuma sauyin darajar naira.

Wani masani kan harkar man fetur, Dr Ahmed Adamu, wanda ke aiki a jami'ar NILE a Abuja, ya ce tashin farashin man da aka samu a makon nan ya faru ne sanadiyyar abu biyu: wato tashin farashin mai a kasuwannin duniya da kuma karyewar darajar naira.

Ya ce "Babban abin da ke tantance farashin man fetur shi ne ainihin farashin da ɗan kasuwa ya saro man kasancewar sau da dama sauran abubuwan ba su sauyawa."

Misali, a watan Yunin 2023, farashin gangar mai a kasuwar duniya ya kasance dalar Amurka 72, kuma ana canza naira a naira 750 kan kowace dala, shi ya sa farashin litar mai a Najeriya ya kama daga naira 479 a birnin Legas.

A watan Yuli kuwa farashin mai a kasuwar duniya shi ne dalar Amurka 80 kan kowace ganga, yayin da ake canza dalar Amurka ɗaya kan kimanin naira 800, shi ya sa farashin litar fetur ya kai 560 a defo.

Sauran abubuwan da ake la'akari da su kafin tantance farashin litar mai su ne kuɗin jirgin ruwa, da kuɗin fito da kuma kuɗin sufuri a cikin Najeriya.

Wani kuma abin mai muhimmanci shi ne ribar da ɗan kasuwa zai sanya, kuma kasuwa ce za ta tantance, sai dai sau da dama ƴan kasuwa ba za su tsuga ribar ba kasancewar za su so su sayar da wuri su sake komawa su ɗauko man.

Akwai yiwuwar farashin mai ya sauka a Najeriya?

Tabbas zai iya sauka, domin kuwa abubuwan da suke sanya farashin man ya ƙaru su ne kuma za su iya sanya shi ya ragu.

A ɓangaren man fetur, yanayin buƙatar man ko rashin buƙatarsa zai iya sauko da farashin litar.

Dr Adamu ya ce "Idan farashin gangar mai ya sauka a kasuwar duniya, ƴan kasuwa za su sayi tataccen man da sauƙi, hakan zai sanya ƴan Najeriya su sayi man cikin farashi mai sauƙi.

"Amma a ɓangaren farashin dalar Amurka kuwa, wannan lamari ne da ya dogara da tsare-tsaren gwamnati."

A halin yanzu dai ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar sun fusata kan ƙarin farashin man fetur ɗin, inda suka yi barazanar ficewa daga tattaunawar da suke yi da gwamnati.

Abin da bai fito fili ba a yanzu shi ne ko gwamnatin za ta sauya matsayinta kan batun na tallafin man fetur.

Source: BBC